Ma’aikatar Harkokin Waje: Ana fatan Sweden za ta girmama addinai daban-daban

Daga CMG HAUSA

A matsayin martani ga babbar tarzoma da ake fuskantar a Sweden, a jiya Laraba a gun taron ‘yan jarida, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya ce ana fatan ɓangaren gwamnatin Sweden ya lura da lamarin da ya faru a matsayin wani darasi, ta yadda za ta fara girmama addinai daban daban, ciki har da Musulunci, da kiyaye halastacciyar moriyar masu bin addinan, da aiwatar da alƙawarin da ya yi na mutuntawa, da kare ‘yancin biyayya ga addinai.

Bisa labarin da aka bayar, a kwanaki baya, wata jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi a ƙasar Sweden ta shirya zanga-zangar adawa da Musulunci, tare da kona littattafan Al-Ƙur’ani a wurare da dama a ƙasar, lamarin da ya haddasa babbar tarzoma daga ɓangaren Musulman da ke zama a ƙasar Sweden, inda aka lalata kayayyakin jama’a, da haddasa jin rauni na wasu mutane da yawa.

Ganin afkuwar lamarin ya sa wasu ƙasashen Musulmai da dama, sun nuna rashin amincewa da takaicinsu ga jakadun ƙasar Sweden a ƙasashen.

Fassarawa: Safiyah Ma