Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Maiden Alex-Ibru, mawallafiyar jaridar The Guardian, ta bayyana a matsayin sabuwar shugabar ƙungiyar Masu Jaridu ta Nijeriya (NPAN), bayan zaɓen da aka gudanar a taron AGM na 2025.
An yi taron ne domin tattauna halin tattalin arzikin ƙasa, tsaro, sauye-sauyen haraji, da kuma makomar dimokuraɗiyya da ’yancin kafafen yaɗa labarai — tare da zaben sabbin jami’ai na ƙungiyar.
A wata sanarwa da Maiden Aleɗ-Ibru tare da Sakatariyar NPAN, Angela Emuwa, suka rattaba hannu, ƙungiyar ta tabbatar da sakamakon taron da aka fitar wa manema labarai a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce, “A zaɓen sabuwar shugabanci: Maiden Aleɗ-Ibru, mawallafiyar jaridar The Guardian, ta zama Shugabar NPAN, yayin da Frank Aigbogun na jaridar BusinessDay ya zama mataimaki.”
NPAN ta yaba wa gwamnatin tarayya bisa aiwatar da wasu muhimman gyare-gyaren tsari, amma ta gargaɗi cewa cire tallafin man fetur da daidaita musayar kuɗin waje sun ƙara raɗaɗin da ake ji a tsakanin talakawa.
ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin ƙasa, jihohi da ƙananan hukumomi su rage kuɗin gudanarwa, su tunkari cin hanci da rashawa, sannan su daidaita hauhawar farashi don rage nauyi a kan jama’a.
