Mafitar Arewa

Spread the love

Duk wanda ya ke kallon cakuɗewar lamura a arewa zai san samun mafita tafiya ce mai tsawo. Dalilai na su ne, ga maciji amma ana nuna igiya, wato yadda duk wani laifi ƙarami ko babba kowa ke kallon kamar sai shugaban ƙasa ko gwamnan jiha ke iya magance shi.

Misali wani abun takaici za ka ji mutum ya fito a kafafe na sadarwa yana faɗin matsaloli wanda abokan zamanmu na kudanci ba haka su ke yi ba. Kuma mu kula hatta a cinikayya a tsakanin shaguna na unguwa da ababe da ba a kai su shago kamar kayan gwari duka waɗanda ke harkar wasunsu kuɗi ne kawai a zukatansu. Ina fatan kowa ya nutsu mu ƙara gane cewa ita fitina ba ta da kaɗan kuma wanda duk ya janwota ya cuci kanshi kuma ya cuci al’umma baki ɗaya. Da fatan mu dinga ƙoƙarin gyara namu kuskuren ta hakan ne za mu samu mafita daga mai iya magance duk wata damuwa shi ne Allah.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa, 07066434519/08080140820.

By ukarofi