Fatan alheri ga Manhaja, yau wasiƙata za ta mayar da hankali ne kan ’yan jaridar Intanet, masu rubutun wallafa labaran ƙarya na hotuna da na bidiyo. Abin haushi da takaicin shi ne mutane ba su tsayawa su tantance labari, kawai sai su rubuta a shafukansu, domin neman mabiya, wasu kuma burinsu shi ne a ce su ne suka fara ba da labarin kuma akasarin labaran na ƙarya ne. Ya kamata mu riƙa sanin irin abubuwan da za mu riƙa sanya wa a shafukanmu, kada jahilci ya riƙa ɗibarmu wajen yaɗa labaran ƙarya ko kuma ɓata wa wani suna. To wai shin mece ce ribarka idan ka wallafa labarin ƙarya a shafinka? Shin ko ka san adadin mutanen da za su ga labarin? Yaya Mutuncinka zai kasance a wurin wanda ya ga labarin daga gare ka kuma daga baya ya gano cewa ba gaskiya ba ne? Saboda haka ya kamata mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu tsaftace yanar gizo, ta hanyar yaƙi da kalaman ɓatanci da labaran ƙarya.
Daga Injiniya Mustapha Musa Muhammad. 09123302968.
