Mahaifiyar ‘yan uku da ke gudun hijira ta nemi taimakon abinci da kuɗi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Wata mahaifiya da aka kora daga gidanta saboda harin ‘yan bindiga, Hindatu Lauwali, wadda ta haifi ‘yan uku, ta yi kira da a taimaka mata da abinci da kuɗi, yayin da jariranta ke karɓar magani na cutar jaundice (yellowness) na jarirai a babban asibitin koyarwa na tarayya (FTH), Birnin Kebbi.
Malama Hindatu, wadda ta haifi maza biyu da mace ɗaya a ranar 25 ga Oktoba, ta yi wannan kiran ne a wata hira da manema labarai garin a Birnin Kebbi a ranar Talata inda ta bayyana cewa ta tsere daga kauyen Ragam bayan harin ‘yan bindiga, yanzu tana zaune a sansanin ‘yan gudun hijira (IDP) a garin Kwargiye a karamar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi.

Ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun mamaye ƙauyen Ragam, suka tilasta mazauna ƙauyen da su gudu.
Ƙungiyar da’awa ta haɗaka ta kai ta ƙaramar hukumar Zuru domin samun ƙarin magani lokacin da rashin lafiyatar ta tsananta.
Ta ce ta haifi jariri na farko da kanta, yayin da aka taimaka mata wajen haifar da sauran biyu a babban asibitin Danko/Wasagu.
A cewarta, ma’aikatan lafiya sun shawarci a kai jariran zuwa babban asibitin Zuru bayan an lura da suna fama da wannan lalurar ta canjin yanayin launin fatar jikin su.

Tare da taimakon mai martaba Sarkin Zuru Alhaji Mika’ilu Sami da na ƙungiyoyin da’awa na haɗaka a Masarautar Zuru, aka kawo ta zuwa FTH, Birnin Kebbi, saboda ‘yan ukun suna buƙatar kulawa ta musamman cikin gaggawa,” in ji ta.

Ta gode wa sarkin, ƙungiyoyin da’awa na haɗaka da reshen Kebbi na ƙungiyar likitocin musulunci ta Najeriya (IMAN) saboda taimakonsu.

Ta bayyana cewa ba ta iya samar da isasshen nono ga jariran, waɗanda yanzu ke buƙatar kulawa ta musamman.
Shugabar IMAN ta Jihar Kebbi, Nurse Khadijat Muhammad, ta ce matar ta haifi ‘yan ukun ta hanyar haihuwa ta al’ada cikin nasara, amma an gano jariran suna da cutar jaundice na jarirai.
Ta ce shugabancin ƙungiyoyin da’awa na haɗaka sun tuntuɓi IMAN don taimakawa a FTH.

“Mun yi ƙoƙarinmu mun taimaka musu, amma bai isa ba saboda muna kuma kula da sauran marasa galihu,” in ji ta.

Mai jinyar ta yi kira ga masu hannu da shuni, ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) da matan gwamnan jiha da su tallafa wa iyalan.

By ukarofi

Leave a Reply