Mai tsaron raga da mataimakin kocin Algeria sun mutu a haɗarin mota

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wani haɗarin mota da ya faru a Algeria ya halaka nai tsaron raga da kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Mouloudia Club El Bayadh lamarin da ya tilastawa hukumar ƙwallon ƙafar aasar ɗage dukkan wasannin da aka tsara bugawa.

Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasar ya ce, mai tsaron ragar ƙungiyar Zakaria Bouziani mai shekara 27 da mataimakin koci, Khalid Muftah sun mutu sanadin haɗarin.

’Yan wasan na hanyar zuwa Tizi Ouzou domin buga wasa da JS Kabylie ranar Juma’a lokacin da motar ɗauke da tawagar ’yan wasan ta yi haɗari kusa da birnin Tiaret da ke Arewa maso yammacin Algeria, a cewar kafafen yaɗa labaran ƙasar.

Shugaban Algeria, Abdelmajid Tebboune ta ce cikin wata sanarwa cewa ya samu rahoton ibtila’in tare da miqa ta’aziyya ga iyalan ‘yan wasan da suka rasa ransu.

Ƙungiyar a saƙon da ta wallafa a shafukan sada zumunta ta ce sauran ’yan wasan da suka ji rauni ba sa cikin wani mummunan yanayi.

A cewar sanarwar, hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar ta yanke shawarar dakatar da duk wasannin da aka shirya yi a ƙarshen mako.