Majalisa ta ƙara wa’adin sa’o’i 48 ga Mataimakin Gwamnan Zamfara ya bayyana a gabanta

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta tsawaita wa’adi da sa’o’i 48 ga Mataimakin Gwamnan Jihar Barr. Mahdi Aliyu Muhammad Gusau, ya bayyana a gabanta don amsa tambayoyi kan zargin aikata ba daidai ba.

Hakan ya biyo bayan ƙudirin da Mataimakin Shugaban Jagoran Majalisar, Hon. Nasiru Bello lawal Bungudu ya gabatar a kan lamarin wan Hon Shafi’u Dama Wanke mai wakiltar mazaɓar Gusau ta biyu (2) a Majalisar ya mara wa baya.

Idan dai za a iya tunawa, ƙudurin da Majalisar ta yanke a ranar Laraba 14 ga watan Yulin 202, ta yanke shawarar gayyatar Mataimakin Gwamnan ya bayyana da kansa tare da Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Hussaini Rabi’u don yi wa Majalisar bayanin dalilin da ya sa ya ba da damar gudanar da gangamin siyasa ga Mataimakin Gwamnan a lokacin da jihar ke juyayin mutuwar mutane sama da 56 da ba su ji ba ba su gani ba a yankin Faru da ke Ƙaramar Hukumar Maradun a jihar sakamakon harin ‘Yan bidiga.

Yayin zaman Majalisar na ranar Talata, Hon. Nasiru Bungudu, ya ce tun da Mataimakin Gwamnan ya samu takardar gayyatar da sammacin Majalisar da ya bayyana ran 27/7/2021 kuma ba a ji wata amsa ko dai daga shi ko ofishinsa ba, har yanzu akwai buƙatar Majalisar ta girmama muƙamin Mataimakin Gwamna sannan a ba shi ƙarin wa’adin awanni 48, wato zuwa ranar Alhamis, 29 ga Yuli, 2021 domin sake amsawa.

Bayan lura da buƙatar da Hon. Bungudu ya gabatar, sai Kakakin Majalisar, Nasiru Mu’azu Magarya, ya yi magana da takwarorinsa kan ko sun amince da tsawaita wa’adin da awanni 48 ga Mataimakin Gwamnan ya bayyana a gaban amajalisar? Lamarin da baki da baki ɗaya ‘yan Majalisar suka amince shi ta hanyar ƙuri’a.

A halin da ake ciki, Darakta Janar na Harkokin Labarai na Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Mustapha Jafaru Ƙaura a wata hira da ya yi da manema labarai jim kaɗan bayan zaman ya ce, Majalisar ta kuma tattauna sosai a kan ƙudirin da zai gyara dokar Hukumar Karatun Alƙur’ani da Haddar Alkur’ani ta Jihar zamfara ta 2005.

Kana ya sake gabatar da ƙudirin a karo na biyu sannan daga baya ya tura shi zuwa ga Kwamitin Majalisar kan Harkokin Addini don bincikowa sannan ya gabatar da rahoton ga zaman majalisar a cikin makonni biyu.