Majalisar dattijai ta amince da ƙudirin N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi , ta hanyar yin gaggawar zartar da ƙudirin dokar da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gabatar mata.
Ƙudirin dokar wanda ya kuma rage lokacin duba mafi ƙarancin albashi daga shekaru biyar zuwa shekaru uku, an yi karatu na ɗaya da na biyu da na uku a jere a zauren majalisar ranar Talata .
Sauran bayanai na zuwa
