Ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, a ranar 13 ga watan Nuwamba 2023, sun bi sahun takwarorinsu na dukkan tashoshin da ke aiki a duniya domin yin shiru na minti daya domin tunawa da ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya da suka rasa rayukansu a yakin da Isra’ila da Hamas ke ci gaba da yi a Gaza.
“Yana da matuƙar baƙin ciki cewa muna tare da dukkan jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya a duk fadin duniya a dukkan tashoshin da ke aiki don yin shiru na minti daya a yau Litinin, 13 ga watan Nuwamba, 2023 don girmama abokan aikinmu da aka kashe a Gaza.”
Muƙaddashin Mazaunin Majalisar Ɗinkin Duniya kuma mai kula da ayyukan jinƙai a Nijeriya, kuma Wakilin Shirin Cigaba na Majalisar Ɗinkin Duniya, Mohamed Yahya, ya bayyana haka a wani taƙaitaccen taro da aka saukar da tutar Majalisar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya a Abuja.
“Kamar yadda kuke gani, an saukar da tutar Majalisar Ɗinkin Duniya zuwa rabin-girma a matsayin alamar girmamawa a wannan taro. “Ina so in nemi dukkan mu da mu yi shiru na tsawon minti daya yayin da muke girmama abokan aikinmu da suka mutu,” in ji shi.
Bugu da ƙari, ya buƙaci duka ma’aikatan da su shiga cikin taron, yana mai jaddada muhimmancin girmama tunawa da waɗanda suka sadaukar da kansu wajen yi wa bil’adama hidima.
Bisa ga ƙa’ida, an kuma yi shiru na minti daya daga ma’aikata 86 da ke halartar taron koli na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya da ke gudana a jihar Neja. Da misalin ƙarfe 1:30 na rana, mahalarta taron sun tashi don yin shiru na minti daya don girmama abokan aikinsu da suka mutu a Gaza.
Bayan shirun minti ɗayan ne, Yahaya ya kammala saƙon nasa da fatan alheri: “Allah ya sa sun huta.”
