Majalisar Dattawa ta amince da ƙudirin dokar kafa ‘yan sandan jihohi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba Majalisar Dattawa ta kammala aiki akan ƙudirin dokar kafa ‘yan sandan jihohi bayan masa karatu na uku, lamarin da ya kawo ƙarshen muhawarar da aka ɗibi tsawon shekaru ana gudanarwa akan tsarin ‘yan sanda domin warware matsalolin taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya.

An cimma nasarar haka ne bayan dogon nazari da kuma da kuma amincewar tabbatar da ƙudirin a dokance daga biyu bisa uku na majalisar.

Haka kuma, an amince da kudirin ne a zaman majalisar ne bayan sanatoci sun yi nazari tare da amincewa da sashe-sashe 26 na kudirin a yayin zaman kwamitin gaba ɗaya.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da tattaunawa kan hanyoyin ƙarfafa tsaro da bai wa jihohi damar taka rawar gani wajen yaƙi da matsalolin tsaro da suka addabi sassa daban-daban na ƙasar.

Ana sa ran ƙarin bayani kan yadda za a aiwatar da tsarin idan ya kammala dukkan matakan da kundin tsarin mulki ya tanada.

By Babaji

Leave a Reply