Majalisar Dattawa ta ba NNPCL, CBN da NDDC sa’o’i 72 su bayyana a gabanta kan zargin coje a rahoton kuɗi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kwamitin Majalisar Dattawa akan Asusun Al’umma, ya bayar da wa’adin kwana uku ga Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Babban Bankin Nijeriya (CBN), Hukumar kula da Ci-gaban yankin Neja-Delta (NDDC), Hukumar kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC) da wasu hukumomi da su bayyana a gabansa sakamakon rashin amsa gayyatarsa a lokuta mabambanta game da warware matsalolin rahotannin kuɗaɗe.

An bayar da wannan umarni ne a ranar Litinin a lokacin da kwamitin ya gabatar da wani zama ba tare da hukumomin sun je gabansa ba kuma babu wani bayani a hukumance game da dalilin rashin zuwan nasu.

Shugaban kwamitin, Sanata Ibrahim Ɗankwambo ya ce, gayyatar hukumomin wani ɓangare na sauke nauyin da aka ɗora musu don tabbatar da gaskiya da adalci a dokance game da al’amarin.

A nasa jawabin, Sanata Babangida Hussaini ya koka game da yadda babu wakilcin ko ɗaya daga cikin hukumomin a yayin zaman, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin girmama Majalisar Dokokin Ƙasa.

Haka ma Sanata Patrick Ndubueze, ya yi kira da a hukunta hukumomin da suka ƙi bayar da haɗin kai akan binciken al’amarin, yana mai cewa kada a sake ba su dama kan rashin bayanin dalilin da ya hana su amsa wa gayyatar kwamitin ba tare da an ɗauki matakin doka akansu ba.

Daga nan ne kwamitin ya ba su wa’adin kwana huɗu na su bayyana a gabansa daga yanzu zuwa ranar 6 ga Agusta, 2026 ko kuma a ɗauki matakin doka akansu.

By Babaji

Leave a Reply