Majalisar Dattawa ta tara wa iyalan malamai da ɗaliban Oyo da aka ceto miliyan N50

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da tara Naira miliyan 50 a matsayin tallafi ga iyalan waɗanda garkuwar makarantun Ƙaramar Hukumar Oriire da ke Jihar Oyo ta rutsa da su a kwanan nan.

Akpabio ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar na yau Laraba, inda ya ce tallafin na da nufin rage wa iyalan da al’amarin ya shafa raɗaɗi.

A cewarsa, za a bayar da Naira miliyan 10 ga kowane ɗaya daga cikin iyalai uku na sojojin da suka rasa rayukansu yayin ceto mutanen, kamar yadda za a ba wa na malamai biyu da suka rasu.

Ya bayyana cewa, an ɗauki matakin ne sakamakon kiraye-kiraye ga majalisar na ta tallafa wa iyalan waɗanda suka rasu da kuma ƙoƙarin jami’an tsaro wajen ceto sauran mutanen da aka sace a wasu sassan ƙasar.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da al’umma suke nuna damuwa akan yadda ayyukan garkuwa da munanan hare-hare suka yawaita a sassan ƙasar.

Da yake jawabi akan al’amarin, Sanata Abdul Ningi, ya yi kira ga shugabancin majalisar da ta tabbatar da cewa an damƙa kuɗaɗen ga waɗanda abin ya shafa, yana mai gargaɗin yunƙurin nuna fifiko ka iya lalata shirin.

By Babaji

Leave a Reply