Majalisar Dattawa ta yi allawadai da kashe mutane 56 a Jihar Neja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Majalisar dattaawa ta yi Alla-wadai da kasha ‘yan Najeriya 56 da sace mata da ƙananan yara a ƙauyen Konkoso da ke jihar Neja inda ta bayyana hakan da lamarin da ba za a lamunta ba.

Wannan mataki na zuwa ne bayan wani ƙuduri na gaggawa da sanatan Neja ta gabas, Sani Musa, ya gabatar a yayin wani zama na gaggawa a ranar Talata.

A yayin da yake gabatar da ƙudurin, ɗan majalisar ya ce, sama da ‘yan jihar 56 ne aka kashe a Konkoso da ke kusa da ƙauyen Pissa a yayin da aka yi garkuwa da mata da ƙananan yara.

Ya kuma yi bayanin cewa, garuruwan da wannan al’amari ya shafa suna iyaka ne da sauran maƙwabtan jihohi wanda ke bai wa ‘yan ta’adda damar zirga-zirga da kai hare-haren.

Musa ya yi gargaɗin cewa yankin Arewa ta tsakiya na fuskantar hare-hare a yankunan karkara da gonaki wanda ke barazana ga samar da wadataccen abinci da bunƙasa tattalin arziƙin na ƙasa da kwanciyar hankali na ƙasa.

Ya kuma yaba wa shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro kan ƙokarin da suke na yaƙi da ta’addanci da irin sadaukarwar da dakarun ke yi a faɗin ƙasar nan.

Sai dai sanatan ya nuna damuwarsa game da harin da ake kai wa ƙauyukan wanda ke nuna giɓin da ke akwai wajen tattara bayanan sirri da haɗin kai da damar ɗaukar matakai da rashin jami’an tsaro a wuraren.

Ya ƙara da cewa garkuwa da mata da ƙananan yara da aka yi ya ƙara ta’azzara matsalar jinƙai da damuwa kan iyalai da tarwatsa al’ummomin.

Musa ya jaddada cewa matuƙar ba a samu sauye-sauye da zamanantar da harkokin tsaro ba, irin wannan hari zai ci gaba da faruwa duk da irin ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi a faɗin ƙasar nan.

A yayin da yake mara wa ƙudurin baya, babban mai tsawatarwa a majalisar, Mohammed Monguno, ya buƙaci a ƙara yawan kasafin kuɗin jami’an tsaro domin magance matsalar.

“A yayin da ake duba kasafin kuɗin tsaro, mun gano cewa babu kuɗin gudanar da manyan ayyuka da aka sakar wa jami’an tsaro.”

“Don haka, kamar yadda yake cikin jawabin shugaban ƙasa na sa dokar ta-ɓaci a ɓangaren tsaro, ya kamata a bai wa jami’an tsaro muhimmanci,” in ji Monguno.

Majalisar dai ta yi zaman alhini na minti ɗaya domin miƙa ta’aziyya ga iyalan da suka rasa makusantansu da kuma al’ummar Neja da gwamnatin jihar.

Majalisar dattawa ta yi kira da a turo ƙarin jami’an tsaro zuwa yankunan da lamairn ya faru domin ƙarfafa ɗaukar mataki da kare harin da ake kai wa al’umma.

Sannan ta buƙaci kwamitin tsaro na rundunar ‘yan sanda da soja (ciki har da na sama) da su duba tsarin tsaro tare da ba da rahoto a cikin makonni 4.

By ukarofi