Majalisar Tarayya na yin kira da a cire jami’o’i daga tsarin biyan wuta na Band A domin rage raɗaɗin kuɗin wuta a kan jami’o’in.
Abubakar Fulata wanda shine shugaban kwamitin majalisar a harkokin jami’o’i ke faɗan haka a yayin wata ziyarar gani da ido da kwamitin ya kai a jami’o’in da ke Arewa maso Gabas.
Ya cigaba da cewa yana da yaƙinin gwamnati za ta saurari wannan kira nasu. A yayin ziyarar sun sami nasarar zuwa jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi da kuma Jami’ar Tarayya da ke Gombe a Kashere.
Sai dai Victor Ogene wanda mamba ne a kwamitin yayi kira da yadda rahaton Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa a Bauchi bai gamsar dasu ba musamman yadda suka kashe kuɗi tsakanin shekarar 2021 zuwa 2023.
Sannan kwamitin ya ja kunnen jami’o’in a kan kashe kuɗin da baya cikin kasafin kuɗi saboda yin haka saɓa wa doka ne.
