
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa wani kwamitin wucin gadi domin tantance Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar.
An ɗauki matakin ne bayan karanta wasiƙar da Abba Kabir Yusuf ya aike wa Shugaban majalisar Jibril Ismail Falgore, a zaman majalisar na ranar Laraba.
Gwamnan ya bayyana cewa ya zaɓi Garo ne bayan tuntuba mai zurfi, yana mai cewa gogaggen ɗan siyasa ne da ya riƙe muƙamai daban-daban, ciki har da shugaban ƙaramar hukuma, shugaban ALGON a jihar, da kuma kwamishina.
Shugaban majalisar ya sanar da kafa kwamitin ƙarƙashin jagorancin manyan shugabannin majalisar domin gudanar da tantancewar cikin gaggawa.
Ana sa ran kwamitin zai gayyaci Garo domin tantance shi, sannan ya miƙa rahotonsa ga zauren majalisar a ranar Litinin.
Gwamnan ya bayyana a cikin wasiƙar cewa ya zaɓi Murtala Garo ne bayan ya gudanar da tuntuɓa mai zurfi, inda ya bayyana shi a matsayin gogaggen ɗan siyasa da ya riƙe muƙaman shugaban ƙaramar hukuma da kwamishina da dai sauransu a matakai daban-daban.
Shugaban majalisar ya sanar da cewa kwamitin, wanda manyan shugabannin majalisar za su jagoranta, yana da alhakin tabbatar da cewa an gudanar da tantancewar cikin gaggawa kamar yadda doka ta tanada.
