Jakadan Nijeriya a Aljeriya, Mahmud Lele ya rasu bayan shekaru 50 a duniya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mohammed Mahmud Lele, wanda shi ne jakadan Nijeriya da aka naɗa zuwa ƙasar Aljeriya, ya rasu bayan shafe shekaru 50 a duniya, kamar yadda rahotanni da dama suka bayyana.

Ma’aikatar Harkokin Waje ta bakin Kakakinta, Kimiebi Ebienfa ta sanar da haka inda ta ce marigayin ya rasu ne a birnin Ankara na ƙasar Turkiyya a ranar 19 ga Afrilu, 2026 bayan fama da jinyar rashin lafiya na tsawon lokaci.

Ta kuma bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga makusantansa da ma Nijeriya baki ɗaya.

Gabanin rasuwar marigayin, an naɗa shi domin wakiltar Nijeriya a ƙasar Aljeriya, saidai bai samu damar fara aiki ba sakamakon rashin lafiyarsa.

Hukumomi sun yi masa addu’ar Allah ya jikansa da rahama, tare da jaddada irin gudunmawar da ya bayar wajen hidimta wa ƙasa.

By Babaji