Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A zaman ta karo na bakwai majalisar zartarwa ƙarƙashin gwamna Dikko Raɗɗa ta amince ta aiwatar da shirin tallafawa ƙananan da matsakaitan kasuwanni (Nano, Micro da Small Enterprises) a manyan hanyoyin jihar, wanda zai tallafa wa ‘yan kasuwa 62,000 a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar.
Wannan shiri na da nufin ba su jarin kasuwa domin bunƙasa kasuwancinsu da inganta rayuwarsu da tattalin arziki a matakin ƙasa.
Haka kuma majalisar ta amince da aikin ginawa da shimfida kwalta a hanyar Rahamawa zuwa Gidan Shehi sai Namadi zuwa Inwala Jan Gefe ta miƙe zuwa Ring Road a cikin birnin Katsina.
Aikin zai inganta ƙarkon hanya, sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a, da kuma bunƙasa harkokin tattalin arziki da ci gaban ababen more rayuwa a yankin.
Harwala yau majalisar ta amince da bayar da kwangilar sayo manyan injina guda 7 domin ginawa, gyarawa da kuma zurfafa madatsun ruwa na ban ruwa (Irrigation Earth Dams) a faɗin jihar. Waɗannan injina za su inganta noman rani, kiwon dabbobi da kamun kifi, tare da samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’umma.
Ta kuma amince da bayar da kwangilar sayo kayan aikin bincike da haƙar ma’adinai a wurare uku (Tama, Tandama da Ƙanƙara) a faɗin jihar. Waɗannan kayayyaki za su bai wa kamfanin bincike da haƙar ma’adinai na Jihar Katsina damar ƙara samun kuɗaɗen shiga da kuma faɗaɗa tattalin arzikin jihar, tare da daƙile hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba wadda ke haddasa matsalolin tsaro a waɗannan yankuna.
Majalisar zartarwa a jihar ta kuma amince da bayar da tallafin jigilar takin zamani na daminar shekarar 2026 domin rabawa manoma a dukkan rumfunan zaɓe 6,652 na jihar. Wannan mataki na daga cikin ƙudirin gwamnati na tabbatar da rarraba taki cikin lokaci, a bayyane, kuma kai tsaye ga manoma, domin kawar da masu shiga tsakani da hana karkatar da taki, tare da tabbatar da cewa takin ya isa ga manoma na gaskiya.
Kan gyaran tsarin ilimin amincewa da almajirai kuwa majalisar ta amince da aiwatar da shawarwarin kwamitin da aka kafa domin gyaran tsarin ilimin almajirai, tsangaya, Islamiyya zuwa tsari na zamani kuma mai ɗorewa.
Daga cikin shawarwarin akwai kafa makarantu huɗu na gwaji (pilot Khalwa Qur’anic model schools) a jihar, daya a kowace shiyya, da kuma makarantar Khalwa ta mata ɗaya a cikin birnin Katsina. Kafa waɗannan makarantu na daga cikin ƙoƙarin wannan gwamnati na gyara da inganta tsarin ilimin almajiranci a jihar Katsina.
