Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Yusuf Muhammadu Buhari, ɗan tsojon shugaban ƙasar Nijeriya, Marigayi Muhammadu Buhari, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Daura/Sandamu/Mai’adua a Jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Yusuf Buhari ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, a gidan gwamnati da ke Katsina. Ziyarar ta samu rakiyar manyan shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya, wakilan al’umma, ’yan uwa da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na mazaɓar.
Jagoran tawagar, Hon. Musa Haro, Hakimin Dumurkul, ya bayyana ɗan takarar a matsayin matashi mai hangen nesa, kishin ƙasa da kuma son kawo sauyi.
Hon. Musa Haro ya kuma yaba wa gwamna Raɗɗa bisa kyakkyawan shugabanci da manufofi masu amfani ga jama’a, yana mai cewa sun ziyarci gidan gwamnati ne domin gabatar da ɗan takarar tare da neman shawarwari, albarka da goyon bayan gwamnan.
Shi ma da yake jawabi, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Musawa/Matazu, Hon. Abdullahi Aliyu General (Dujiman Katsina), ya bayyana cikakken amincewarsa da ƙwarewar Yusuf Buhari wajen bayar da wakilci nagari. Ya jaddada muhimmancin haɗin kai a cikin APC tare da kira ga ’ya’yan jam’iyya da masu ruwa da tsaki da su mara wa nagartattun ’yan takara baya domin ci gaba da nasarorin jam’iyyar.
A nasa jawabin, Hon. Fatihu Muhammad, darakta-janar na hukumar kula da ingancin irin noma ta ƙasa (National Agricultural Seeds Council) kuma ɗan uwan ɗan takarar, ya bayyana tarihin Yusuf Buhari, gogewarsa da kuma shirinsa na yi wa al’umma hidima. Ya ce wannan mataki ya samo asali ne daga hangen nesa na ƙarfafa matasa, inganta cigaban karkara da kuma walwalar al’umma gaba ɗaya.
Wakilan al’umma daga mazabar Daura/Sandamu/Mai’adua suma sun bayyana goyon bayansu ga wannan buri, inda suka bayyana Yusuf Buhari a matsayin wani tsani tsakanin tsofaffi da matasa da kuma alamar sabon fata. Sun yi alƙawarin cikakken goyon baya tare da kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su haɗa kai domin samun nasara da ci gaba.
Minister Al’adu da Tattalin Arzikin Kirkira, Barr. Hannatu Musa Musawa, a nata jawabin, ta yabawa Yusuf Buhari kan fitowa takara domin yi wa jama’a hidima. Ta jaddada muhimmancin shigar matasa cikin harkokin shugabanci tare da bayyana wannan buri a matsayin da ya dace da zamani, wanda ke nuni da sabon salo na shugabanci da ya maida hankali kan ƙirƙire-ƙirƙire, haɗin kai da ci gaban ƙasa. Ta kuma ƙarfafa ci gaba da tuntuɓa da jama’a tare da bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya.
Da yake mayar da martani, Gwamna Raɗɗa ya yabawa Yusuf Muhammadu Buhari kan aniyarsa na yi wa al’ummar Jihar Katsina hidima. Ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na tabbatar da adalci da gaskiya da haɗin kai a cikin jam’iyyar APC.
Gwamna Raɗɗa ya shawarci ɗan takarar da ya kasance mai juriya, ya ci gaba da tuntuɓar jama’a, tare da kiyaye tawali’u da gaskiya a cikin siyasa. Haka kuma ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na jam’iyya da su fifita zaman lafiya, haɗin kai da adalci ga duka yan takara yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
Wannan ziyara na nuni da ci gaba da tattaunawar siyasa a cikin APC tare da ƙara bayyana yadda harkokin siyasa ke ƙara ƙarfi gabanin zaɓen shekarar 2027 a Jihar Katsina.
Mahalarta taron sun haɗa da kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Rt. Hon Nasir Yahya Daura, Ministar Al’adu, Barr Hannatu Musawa, Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Barr. Abdullahi Garba Faskari, Zarah Buhari, manyan jami’an gwamnati, mambobin majalisar zartarwa ta jiha, yan uwa da abokan arziki, da sauran masu ruwa da tsaki.
