Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta fara shirye-shiryen tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, daga muƙaminsa bisa zargin almundahanar kuɗi.
Matakin ya biyo bayan zarge-zargen da ake masa na badaƙala a harkokin kuɗi, wanda majalisar ta ce ya saɓa da dokokin da suka shafi gudanar da mulki.
Jagoran masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala ne, ya gabatar da takardar ƙudirin tsige shi a zauren majalisar.
Ya ce, an ɗauki matakin ne bisa tanadin Sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima).
Dala, ya ce zarge-zargen sun shafi lokacin da Abdussalam ya riƙe muƙamin Kwamishinan ƙananan Hukumomi tsakanin 2023 zuwa 2024, da kuma lokacin da yake riƙe da mataimakin gwamna.
A lokacin da yake Kwamishinan ƙananan Hukumomi 44 na jihar, ya ce Abdussalam ya riƙa karɓar Naira miliyan 1.5 a kowane wata daga kowace ƙaramar hukuma tsakanin Yunin 2023 zuwa Janairun 2024, wanda ya kai Naira miliyan 66 a wata, jimillar Naira miliyan 462.
Haka zalika, ya ce tsakanin Fabrairu zuwa Yulin 2024, kowace ƙaramar hukuma ta sake biyan mataimakin gwamnan Naira miliyan 3.255 a wata da sunan gudanar da wasu ayyuka na musamman, wanda ya kai kusan Naira miliyan 726 a tsawon watanni shida.
Dala, ya kuma zarge shi da amfani da muƙaminsa wajen sa ƙananan hukumomi 44 su biya wani kamfanin NovoMed Pharmaceuticals Limited, Naira miliyan 10, wanda ya kai jimillar Naira miliyan 440.
Ya ce, lamarin ya saɓa da dokokin saye da gudanar da kuɗaɗen gwamnatin jihar. Ya ce, waɗannan zarge-zarge manyan laifuka ne a ƙarƙashin kundin tsarin mulki, kuma sun saɓa da amana da ƙa’idojin da ake buƙata daga jami’in gwamnati.
Dala, ya ƙara da cewa ’yan majalisa 38 ne suka sanya hannu kan ƙudirin tsige mataimakin gwamnan, wanda ya cika sharaɗin da kundin tsarin mulki ya gindaya domin fara aiwatar da tsari.
Shugaban majalisar ya amshi takardar ƙudirin, kuma ana sa ran zai miƙa ta ga mataimakin gwamnan bisa tsarin doka.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, mataimakin gwamnan bai fitar da wata sanarwa ba dangane da zarge-zargen.
