Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo ya musanta jita-jitar da aka fara yaɗawa cewa ya yi bankwana da duniya.
A ’yan kwanakin nan ne aka fara yaɗa wani rubutu da ke nuna cewa Obasanjo ya mutu, kuma kafin ya bar duniya ya rubuta wata takarda game da mutuwarsa.
Tsohon shugaban ƙasar, ya kuma sake bayyana damuwarsa kan matsalar shugabanci da ke hana ci gaban ƙasashen Afirka, yana mai cewa gazawar shugabanni ita ce babbar matsalar da ta jefa nahiyar cikin talauci, rikice-rikice da rashin ci gaba tsawon shekaru.
Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin wani taron tattaunawa na musamman da aka shirya domin murnar cikarsa shekaru 89 da haihuwa a garin Abeokuta.
Taron, mai taken “Nauyi da Albarkar Jagoranci: Tunani daga Afirka zuwa Duniya”, ya zama wani dandali da tsohon shugaban ya yi bayani mai zurfi kan matsalolin shugabanci a nahiyar.
Ya jaddada cewa Afirka ba wata matsala ba ce da ake ƙoƙarin sarrafawa kawai, a maimakon haka alƙawari ce da ya kamata a cika ta hanyar nagartaccen shugabanci mai gaskiya, jajircewa da kuma rashin cin hanci.
A cewarsa, duk da irin albarkatun da Afirka ke da su na ƙasa, arziki da jama’a, nahiyar ta kamata ta kasance cikin zaman lafiya, wadata da tasiri a duniya. Sai dai, a zahiri har yanzu sassa da dama na nahiyar na fama da talauci, cututtuka, yunwa, rikice-rikice da rashin tsaro.
Tsohon shugaban ya ce babbar matsalar ba ta samo asali daga yanayin ƙasa ko tarihin nahiyar kaɗai ba, sai dai gazawar shugabanni da aka dora musu amanar mulki amma suka ƙasa yi wa al’umma hidima yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa sau da yawa sabbin shugabanni kan zo da alƙawuran gyara da ci gaba, amma daga baya su fara amfani da mulki domin amfanin kansu, iyalansu ko kuma jam’iyyunsu. A cewarsa, wasu daga cikinsu ma kan murde dimokuraɗiyya, su raunana cibiyoyin gwamnati, su hana ’yancin jarida, ko su tsoratar da ɓangaren shari’a da ƙungiyoyin farar hula.
Obasanjo ya yi kira ga ƙasashen Afirka da su mayar da hankali kan gina shugabanci nagari, ba wai koyar da shugabanci kaɗai ba. A cewarsa, dole ne a samar da shugabanni da aka gina da ɗabi’u da ƙima na gaskiya da adalci domin su iya tafiyar da al’umma yadda ya kamata.
Ya kuma jaddada cewa makomar Afirka tana hannun matasa. Ya ce nahiyar na da yawan matasa sosai, wanda hakan zai iya zama babbar dama ta cigaba ko kuma babbar barazana idan ba a kula ba.
A cewarsa, rashin ilimi da rashin aikin yi ga matasa na iya haifar da matsaloli masu tsanani, yana mai tunatar da cewa sama da yara miliyan 24 a Nijeriya da ya kamata su kasance a makaranta ba sa zuwa makaranta. Ya yi gargaɗin cewa hakan na iya zama wata hanya ta samar da sabbin mambobin ƙungiyoyin ta’addanci ko ’yan bindiga a nan gaba.
Tsohon shugaban ya kuma yi bayani kan nauyin da shugabanci ke tattare da shi, yana mai cewa daya daga cikin manyan nauyin shi ne kadaici wajen yanke hukunci. A cewarsa, sau da yawa shugaba ne kadai ke daukar hukuncin da zai shafi rayuwar miliyoyin mutane.
Ya tuna da lokacin da yake kwamandan rundunar Third Marine Commando Division a karshen Yaƙin Basasa na Nijeriya a shekarar 1970, inda ya ce ya dauki wani muhimmin hukunci na soja da ya taimaka wajen ceton rayukan fararen hula.
Obasanjo ya kuma bayyana cewa wani nauyi na shugabanci shi ne yadda jama’a ke dora manyan fata a kan shugaba. Ya ce lokacin da aka zabe shi Shugaban ƙasa a shekarar 1999, bayan shekaru na mulkin soja, mutane da dama sun yi tsammanin zai kawo sauyi cikin gaggawa kamar mu’ujiza.
Sai dai ya ce duk da irin waɗannan ƙalubale, shugabanci na dauke da albarka, musamman damar yi wa jama’a hidima da kawo sauyi mai ma’ana. Ya ambaci yadda gwamnatin sa ta samu sassaucin bashin Paris Club, wanda ya ba Nijeriya damar zuba jari a fannoni kamar makarantu, asibitoci da manyan ayyukan more rayuwa.
Haka kuma ya tuna da kafa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, wacce aka kafa domin daƙile satar dukiyar ƙasa da kuma mayar da ita ga jama’a.
Obasanjo ya kuma yi magana kan yadda aka tsare shi a gidan yari na tsawon shekaru uku da rabi a zamanin mulkin soja na marigayi Janar Sani Abacha, bayan abin da ya kira shari’ar karya. Ya ce wannan ma wani ɓangare ne na nauyin shugabanci.
A ƙarshen jawabinsa, tsohon shugaban ya mayar da martani ga wasu jita-jita da ake yaɗawa cewa ya mutu, yana mai cewa wasu na yaɗa wata takardar ƙarya da aka danganta da shi wadda ke sanar da mutuwarsa.
Ya ce, irin waɗannan mutane suna ɓata lokacinsu ne kawai domin a cewarsa har yanzu yana cikin ƙoshin lafiya kuma Allah Yana da wasu ayyuka da ya tanada masa a duniya.
Obasanjo ya ce, Allah ne ya kiyaye shi har zuwa yanzu kuma ya ba shi ƙarfi da lafiya domin ci gaba da hidima ga al’umma.
