Majalisar Wakilai za ta binciki saɓanin matatar Dangote da ’yan kasuwar mai

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A ranar Laraba ne kwamitin Majalisar Wakilai mai Kula da Albarkatun Man Fetur ya kammala shirye-shiryen sake buɗe bincike kan yadda aka samu OɓH Energy, da ƙorafe-worafen da ma’aikatan kamfanin NNPC suka yi, inda ya nuna cewa majalisar ta yi watsi da rahoton binciken da aka yi tun farko kan lamarin, wanda hakan ya sa aka sake ɗaukar sabon mataki.

Kwamitin yayin da yake sanar da cewa zai kuma gudanar da bincike kan matsalolin da ke da alaƙa da samun ɗanyen mai daga matatun gida da na zamani, da kuma dalilin da ya sa masu tace matatun gida za su yi tafiya zuwa ƙasar Switzerland maimakon samun ɗanyen mai a cikin gida, ya ce zai binciki maƙudan kuɗaɗen da aka kashe a cikin tsarin ‘Turn Around Maintenance’ na manyan matatun ƙasar da kuma dalilin da ya sa aikin bai samar da sakamakon da ake so ba.

A yayin da yake magana a wani taron manema labarai, shugaban kwamitin, Hon. Ikenga Ugochinyere, ya ce abin takaici ne yadda bayan hatsaniya da aka yi na dawo da matatun mai na Fatakwal da Warri, sun sake rufewa.

“Ba mu fito don kare kowa ba, idan aka samu wani da aikata cin hanci da rashawa, to a bar doka ta ɗauki mataki,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, kwamitin zai kuma binciki batun shigar da masu aikin haƙo ma’adinai a cikin harkar tace man fetur.

Ya ce, kwamitin ya yanke shawarar yin watsi da buƙatar da ke neman a rusa hukumar NMDPRA saboda PIA ce ke ba shugaban ƙasa ikon naɗawa, ya wara da cewa, “ba za mu iya komawa kan tsohon tsarin da kowace gwamnati ke korar mutane ba yadda ta ke s

By ukarofi