Makomar ilimi a duniya za ta ta’allaƙa da yanar gizo – Shugaban NOUN

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Jami’ar Karatu Daga Gida ta Nijeriya (NOUN), Farfesa Olufemi Peters, ya bayyana cewa tsarin Koyo Daga Gida (ODL) ya kasance makomar ilimi a duniya.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake rantsar da sabbin ɗalibai 23,344 da suka yi rajistar karatun digiri daban-daban, digirin digirgir da digiri na uku. 

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na NOUN, Ibrahim Sheme ya sanya wa hannu a ranar 8 ga Janairu, 2025, ya ce Peters na magana ne a wajen bikin ɗaukar sabbin ɗalibai karo 27, inda ya tarbi sabbin ɗaliban jami’ar.

Bikin wanda aka gudanar a cibiyoyin karatu na NOUN a duk faɗin ƙasar, ya kuma shaida rantsuwar sabbin ɗalibai.

Shugaban jami’ar ya bayyana ikon tsarin ODL wajen daidai tsarin ilimi a duniya.

Peters ya nanata ƙudirin NOUN na kawo sauyi a fannin ilimi a Nijeriya, yana mai bayyana tsarin ODL a matsayin makomar ilimi, musamman a wannan zamani na ƙirƙire-ƙirƙire na dijital.

Ya ce: “tsarinmu yana baibwa ɗalibai damar koyo a lokutan kansu, inda za su iya haɗa karatu tare aiki da ɗaukar nauyin iyali.

“NOUN tana cike giɓin samun ingantaccen ilimi, tare da tabbatar da haɗin kai ga dukkan ‘yan Nijeriya, ba tare da la’akari da shekaru, wuri, ko yanayi ba.”

Da yake ba da cikakken bayani kan sabbin ɗalibai 23,344 a tsangayar darussa tara, ya ce jimillar 18,106 ne suka yi rajistar karatun digiri na farko, yayin da 5,196 suka yi karatun digiri na biyu.

Magatakardar NOUN, Mista Oladipo Ajayi, shi ne ya rantsar da ɗaliban.

By ukarofi