Tinubu ya kori Shugabar Jami’ar Abuja, Aisha Maikudi, da yin wasu canje-canje a jami’o’i

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rusa majalisar gudanarwa ta Jami’ar Abuja, wadda a yanzu ake kira da Jami’ar Yakubu Gowon, ya kuma sauke Farfesa Aisha Sani Maikudi daga muƙamin Mataimakiyar Shugabar Jami’ar.

Bayo Onanuga, mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, a cikin wata sanarwa ya ce, “Shugaban ya kuma sanar da sauye-sauyen shugabanci a jami’o’in gwamnatin tarayya da dama”.

A cewar sanarwar, “Bugu da ƙari, Shugaba Tinubu ya tsige Farfesa Polycarp Emeka Chigbu daga muƙaminsa na muƙaddashin mataimakin shugaban jami’ar Nijeriya, Nsukka (UNN), kafin wa’adinsa ya ƙare a ranar 14 ga watan Fabrairu.”

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da sauye-sauyen shugabanci a jami’o’in gwamnatin tarayya da dama, ciki har da Jami’ar Abuja, wadda a yanzu ake kira da Jami’ar Yakubu Gowon.

Waɗannan canje-canjen za su aiki ne nan take.

A jami’ar Yakubu Gowon, Shugaba Tinubu ya rusa majalisar gudanarwar baki ɗaya tare da sauke Farfesa Aisha Sani Maikudi daga muƙamin mataimakiyar shugabar jami’ar.

Sanata Lanre Tejuoso, wanda a halin yanzu Pro-Chancellor na Jami’ar Aikin Gona ta Makurdi ne aka naɗa shi a matsayin Pro-Chancellor na Jami’ar Yakubu Gowon. Sanata Joy Emordi, wacce a yanzu ita ce shugabar jami’ar ilimi ta Alvan Ikoku za ta gaje shi a Makurdi.

Domin ya gaji Maikudi, Shugaba Tinubu ya naɗa Farfesa Lar Patricia Manko a matsayin muƙaddashin mataimakin shugaban jami’ar Yakubu Gowon na tsawon watanni shida. Ba za ta cancanci neman takamaiman matsayin Mataimakin Shugaban Jami’ar ba idan ta samu.

Bugu da ƙari, Shugaba Tinubu ya tsige Farfesa Polycarp Emeka Chigbu daga muƙaminsa na mataimakin Shugaban jami’ar Nsukka (UNN), kafin wa’adinsa ya kare a ranar 14 ga watan Fabrairu.

An nada Farfesa Oguejiofu T. Ujam a matsayin magajinsa na tsawon watanni shida kuma ba zai cancanci neman muƙamin na dindindin ba.

Canje-canjen shugabanci a UNN ya kai matsayin Pro-Chancellor, inda Gen. Ike Nwachukwu ya koma Pro-Chancellor a Jami’ar Uyo. Shugaba Tinubu ya naɗa Injiniya Olubunmi Kayode Ojo a matsayin sabon shugabar UNN. A baya, Ojo ya riƙe wannan matsayi a Jami’ar Tarayya ta Lokoja da Jami’ar Tarayya ta Oye-Ekiti.

Farfesa Zubairu Tajo Abdullahi, wanda a halin yanzu shi ne Pro-Chancellor na Jami’ar Uyo, an naɗa shi ya gaji Ojo a Jami’ar Tarayya ta Lokoja.

Sanata Sani Stores shi ne sabon Shugaban Jami’ar Ilimi ta Alɓan Ikoku, wanda ya gaji Sanata Joy Emordi. Sanata Stores ɗan majalisa ne a Jami’ar Nijeriya, Nsukka.

Bugu da ƙari kuma, Barista Olugbenga Kukoyi, wanda ɗan majalisa ne a jami’ar Nijeriya, Nsukka, an naɗa shi a matsayin sabon Shugaban Jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Awka a jihar Anambra.

Duk alƙawura da yanke shawara na sake aiki suna aiki nan take.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa, waɗannan sauye-sauyen na nuni da ƙudirin gwamnatinsa na farfaɗo da harkar ilimi mai zurfi a Nijeriya ta hanyar jagoranci da riƙon amana.

Sake fasalin yana da nufin ƙarfafa shugabanci da ƙwararrun ilimi a cikin ɓangaren ilimin manyan makarantun Nijeriya.

By ukarofi