Bayan shekara bakwai ’yan Jihar Nasarawa 200,000 da suka rasa matsugunansu sun koma gida

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shekaru bakwai bayan da ƙungiyar ‘yan ƙabilar Egbura ta kori ’yan ƙabilar Bassa sama da 200,000 a ƙaramar Hukumar Toto a jihar Nasarawa, ’yan asalin ƙabilar za su koma gidajen kakanninsu a ranar 10 ga watan Fabrairu.

Wannan ci gaban ya biyo bayan wasu tarurrukan zaman lafiya da gwamnatin jihar da shugabannin hukumomin tsaro suka shirya a jihar.

Shugaban riƙo na ƙungiyar Zaman Lafiya ta Matasan ƙabilar, Joshua Gomina, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce, ‘yan uwansa sun yi gudun hijira tun ranar 22 ga Afrilu, 2018, lokacin da rikicin ƙabilanci ya ɓarke da Egburas.

Gomina ya yaba wa gwamnatin jihar da jami’an tsaro da kuma ƙaramar hukumar bisa ƙoƙarin da suka yi na ganin an shawo kan matsalar.

“Mun yi farin cikin sanar da mu a hukumance cewa ranar Litinin 10 ga Fabrairu, 2025, an shirya dawowar al’ummar Bassa da suka yi gudun hijira a ƙaramar hukumar Toto ta Jihar Nasarawa.

“Tun a shekarar 2018 al’ummar Bassa ke fuskantar ƙalubale da dama a sakamakon rikicin ƙabilanci da ya faru da ƙabilar Egbura.

“Yawancin mutanen Bassa da suka rasa matsugunnansu a cikin al’ummomin da ke kewayen sun haura 200,000 kuma muna fatan da yawa daga cikin mutanen da suka rasa matsugunansu za su koma gidajen kakanninsu mako mai zuwa Litinin 10 ga Fabrairu, 2025,” inji shi.

Gomina ya ci gaba da cewa gwamna Abdullahi Sule ya baiwa kwamandan runduna ta 177 Guard Battalion da keffi da shugaban aaramar hukumar Toto Ahmad Yahaya damar sa ido akan yadda al’ummar Bassa da suka rasa matsugunansu za su koma garuruwan kakanninsu.

Ya ƙara da cewa, ga waɗanda suka dawo daga Legas, Ibadan, Kaduna da Lokoja, wurin taron zai kasance a ƙauyen Kekeshi, a karamar hukumar Abaji, babban birnin tarayya, Abuja.

Waɗanda suka dawo daga Benuwai, Filato, da Lafia za su haɗu a ƙauyen Gunki da ke ƙaramar hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawa.

“Dangane da wannan ci gaba, muna kira ga duk ‘yan ƙabilar Bassa da suka yi gudun hijira daga ƙaramar hukumar Toto da ke zaune a faɗin ƙasar nan da su shirya komawa gida.

“Muna kuma miƙa goron gayyata ga hukumar kula da ‘yan gudun hijira da baƙin haure da ‘yan gudun hijira ta ƙasa; Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar ɗinkin Duniya; Ma’aikatar Agaji, Gudanar da Bala’i da Ci gaban Al’umma; Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa; ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu; da sauransu, don tallafa wa ‘yan Bassa da suka dawo da duk wani taimako da za su iya bayarwa,” inji shi.

By ukarofi