Malamai sun tsunduma yajin aiki a Neja

Daga UMAR M. GOMBE

Malaman makarantun gwamnati a jihar Neja sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a wannan Laraba.

Cikin wata takardar sanarwa wadda Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa (NUT) reshen jihar ta fitar cikin daren da ya gabata, NUT ta ce malaman firamare da na sakandare na gwamnati a jihar, sun soma yajin aikin ne saboda gazawa da gwamnatin jihar ta yi wajen biya wa malamai buƙatunsu kamar yadda aka yi yarjejeniya a baya.

NUT ta ce kafin kai wa ga ɗaukar wannan mataki sai da ta tattauna da Shugaban Ma’aikata na jihar da manyan sakatarori a ranar 4 ga Mayu, 2021 don neman mafita amma taron ya gagara haifar da ɗa mai ido.

Da wannan ne NUT ta ce ta bada umarnin a rufe duka makarantun firamare da na sakandare da ke faɗin jihar, sannan malamai kowa ya zauna a gida, daga Laraba, 5 ga Mayu, 2021.

Kazalika, NUT ta umarci jagororinta da rassan ofisoshint da AOPSHON da ANCOPSS da su tabbatar da mambobinta sun martaba wannan mataki da aka ɗauka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *