Malaman jami’a su na rara-gefen koma wa yajin aiki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Alhamis da ta gabata Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Nijeriya ASUU ta koka kan yadda Gwamnatin Tarayya ta kasa cika mata alƙawarin da aka daɗe ana kai ruwa rana tsakanin ƙungiyar da gwamnati. Lamarin da ya sa ƙungiyar ASUU ta fara rara-gefe da barazanar komawa yajin aiki. 

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa Ƙungiyar Malaman Jami’a ASUU tana cewa har zuwa yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta ce komai ba game da buƙatun da suke nema daga gareta bayan shafe sati uku da suka gindaya.

Kwadinetan ƙungiyar ta ASUU, Dr. Salahu Lawal shi ne ya shaida hakan a wani taron manema labarai da suka kira a Abuja jiya Alhamis, inda ya bayyana cewa alamu sun nuna gwamnati na so ƙungiyar ta su ta ƙara tsunduma cikin wani yajin aikin.

Ya bayyana cewa gwamnati tana yin hakan ne kawai don ta manta da buƙatunmu da ke ƙasa, waɗanda muka yi yarjejiniya da ita tun a watan Disambar shekarar 2020 da kuma wanda aka ƙulla a Fabrairun 2019.

A cikin jami’io’in da abun ya shafa sun haɗa da Jami’ar Tarayya da ke Lafiya da Jam’iar Kimiyya da Fasaha da ke Minna da Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi da Jami’ar Ibrahim Badamasi Babagida da ke Lapai, sai kuma Jami’ar Abuja.

“Ƙungiyar mu ta yi yarjejiya da gwamnati cikin ruwan sanyi, inda gwamnati ta buƙaci ASUU da ta janye yajin aiki da take yi, amma gwamnati ta kasa cika mana alƙawari.

“Fiye da shekara guda kenan bayan qungiyar mu ta janye dogon yajin aiki na tsawon watanni tara, amma har yanzu gwamnatin tarayya ta ƙi yin wani abu akan buƙatun mu,” inji shi. 

“Aiwatar da dukkan buƙatun mu da suke ƙasa na watan Fabrairun 2021 tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU.

“Gaggauta aiwatar da tsari sana’o’in ƙungiyar ASUU da a aka jibge don bunƙasa arzikin jama’a da kuma samun wani hasafi wanda ake kira da UTAS. 

“Biyan dukkan kuɗaɗen da muke bin gwamnati na harkokin karantu da ake kira ‘Earn Academin Allowance’ a turance (EAA) da kuma kuɗaɗen ariyas na qarin girma.

“Gaggauta fitar da rahoton ziyarar kwamitin shugaban ƙasa zuwa jami’o’in gwamnatin tarayya 2021.
“Gaggauta ɗaukar mataki a kan kwamitin da ke kula da harkokin jami’o’in jihohi,” inji Lawal.

Kamar yadda ya bayyana, ya ce cimma waɗancan buƙatu da ya zayyana, su ne kawai za su iya daidaita al’amura tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya har ɗaliban jami’a su samu damar ci gaba da ɗaukar karatu.

Lawal ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su karfafa wa gwamnati gwiwa wajen mutunta yarjejeniyar da ƙungiyar ta yi da ita domin guje wa irin waɗannan matsaloli a jami’o’in ƙasar nan.