Yadda bayyanar Omicron ke barazana ga walwalar ’yan Nijeriya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Duk da tallafin da gwamnatin tarayya ta ce tana bayarwa don rage raɗaɗin talauci da karayar tattalin arziki ga wasu ’yan Nijeriya, sakamakon tasirin da annobar COVID-19 ta haifar ga rayuwar miliyoyin al’ummar ƙasar nan da harkokin su, har yanzu rayuwar wasu da dama ba ta koma daidai ba.

Sai a makon da ya gabata ne, a hukumance Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin ma’aikatan gwamnati da ke matakin albashi na 12 zuwa ƙasa su koma bakin aikin su, bayan shafe tsawon watanni takwas suna aiki daga gida, kamar yadda gwamnati ta ba da umarni, domin daƙile yaɗuwar annobar Korona a tsakanin ’yan Nijeriya.

Tun da aka shiga ƙuncin rayuwa da hauhawar farashin kayan masarufi a kasuwanni, rayuwar akasarin al’ummar ƙasar nan ta shiga wani hali matsananci, duk a dalilin da ake danganta shi da matakan da hukumomi suka riƙa ɗauka don daƙile yaɗuwar cutar.

Kamar wannan halin da jama’a ke ciki bai isa ba, yanzu kuma an fuskanci wata sabuwar barazana da ke tunkarar ba Nijeriya kaɗai ba har ma da duniya.

Bayyanar sabon nau’in cutar Korona daga ƙasar Afrika ta Kudu wanda aka yi wa laƙabi da Omicron ta fara ɗaga hankalin mahukunta, kamar yadda rahotanni ke bayyana cewa, kimanin ƙasashe 40 ne aka samu bayyanar wannan nau’in cuta, ciki har da Nijeriya. Yayin da a cikin wannan mako mai ƙarewa Babban Daraktan hukumar yaƙi da yaɗuwar cututtuka ta ƙasa ta NCDC Ifedayo Adetifa ya sanar da samun ƙaruwar mutane uku a Nijeriya da suka kamu da nau’in cutar Omicron, wanda ya kai adadin su zuwa shida.

Wannan al’amari ne mai matuƙar ɗaga hankali, musamman ganin halin rayuwar da ’yan Nijeriya da dama ke fuskanta, tun daga ƙalubalen tsadar rayuwa, taɓarɓarewar tsaro, da rashin samun kyakkyawan jagoranci. Idan har aka ce za a qara ɗaukar wasu matakai a kan jama’a, a wannan hali, gaskiya abu ne da zai kaɗa hantar cikin kowanne ɗan ƙasa, lura da yadda rayuwar ke daɗa zama mara tabbas.

Rahotanni sun rawaito Ministar kula da kasafin kuɗi da tsare-tsaren ƙasa, Zainab Ahmed tana faɗa a wajen babban taron ƙasa kan cutar COVID-19 da aka gudanar a Abuja cewa, kimanin ’yan Nijeriya Miliyan 11 ne za su shiga matsanancin talauci cikin shekara mai zuwa, sakamakon matakan da za a ɗauka game da tasirin wannan annoba.

Subhanallah! Wannan masifa da yawa take!! Da wanne talaka zai ji? Hakan fa na zuwa ne makonni bayan rahoton da aka riƙa yaɗawa na cewa, idan gwamnati ta cire tallafin da ake bayarwa kan shigo da tataccen man fetur, wanda masana tattalin arziki suka bayyana cewa hakan zai ƙara tsananta halin da tattalin arzikin ƙasar nan ke ciki. Saboda ƙarin farashin man fetur zai iya sa farashin kayan abinci da duk wani abin buƙata ya yi hauhawar da ba a taɓa tsammani ba.

Tun yanzu ma, wasu gwamnatocin ƙasashen Turai sun fara dakatar da Matafiya daga wasu ƙasashen Afirka shiga ta jirgin sama, kamar yadda sanarwa ta baya bayan nan wacce ta fito daga gwamnatin Birtaniya ke sanar da hukumomi a Nijeriya cewa, an gano wasu matafiya su 7 da suka fito daga nan ƙasar suna ɗauke da nau’in cutar Omicron, abin da ya sa gwamnatin ƙasar dakatar da duk wani matafiyi daga Nijeriya shiga ƙasar ta jirgin sama, umarnin da ya harzuƙa ’yan Nijeriya da dama, musamman ma waɗanda ke shirin tafiya hutun Kirsimeti da na Sabuwar Shekara.

Ya kamata tun yanzu mahukunta a ƙasar nan su sake tashi tsaye bayan hutun rabin lokaci da suka tafi ganin cewa, kamar an ci galabar cutar Korona a duniya, domin samar da ingantattun matakan da suka dace, wajen tunkarar wannan mummunan al’amari, musamman a ɓangaren inganta kiwon lafiya, samar da magungunan rigakafi da kayayyakin aiki. Don kauce wa fargar jaji, sakamakon sakaci daga hukumomi kamar yadda aka saba gani a ƙasar nan.

A ƙasa kamar Nijeriya, inda ake da yawan mutane fiye da miliyan 2000, lallai ya kamata hukumomi su ƙara ƙaimi, don shawo kan matsalolin da za a iya fuskanta a gaba, alhalin ba a gama fita daga wanda ake ciki ba. Kama daga ɓangaren kiwon lafiya, harkokin ilimi, zuwa tattalin arziki da tsaro.

Abubuwan da suka faru tun da farko yayin tsanantar da annobar ta yi a Nijeriya da duniya baki ɗaya sun kamata su zama mana darasi. Ba matsalar rabon kuɗi ko ba da tallafi ba ne, al’amari ne da ke buƙatar nuna shugabanci nagari, amfani da ƙwarewa da dabaru na zamani wajen tunkarar koma mai zai iya faruwa. Ya kamata a ce yanzu an waye da matakan da suka dace wajen daƙile yaɗuwar wannan annoba.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ɗauki wasu tsauraran matakai don shawo kan yaɗuwar cutar da ke daɗa hauhawa a jihar kusan fiye da ko ina a faɗin ƙasar nan. Yayin da aka tsananta game da matakan rigakafi, da yin alluran kariya, don yaƙi da annobar ga dan gadan. Yanzu haka ma ya umurci Ma’aikatar lafiya ta jihar ta tabbatar ta yi wa mutane Miliyan 4 alluran rigakafi, kafin nan da ranar Kirsimeti, wato 25 ga Disamba, 2021. Da kuma hana mutane shiga wajen tarukan jama’a ba tare da shaidar rigakafin su ba.

A maimakon wasu baragurbin shugabanni da ma’aikatan lafiya su riƙa amfani da wannan dama wajen arzurta kansu da wawure kayan aikin da gwamnati ke samar wa, kamata ya yi a riqa la’akari da irin haɗarin da ƙasar nan ke ciki, da wanda jama’a za su shiga, matuqar aka yi wa wannan al’amari riƙon sakainar kashi.

Mu ma kuma ’yan ƙasa, ya kamata mu ɗauki darasi daga abubuwan da suka faru da mu, waɗanda suka haifar da rufe kasuwanni, makarantu, wuraren ibada, da ma hana zirga zirga baki ɗaya, domin idan damuwar ta tashi zuwa a kan mu talakawa za ta ƙare, a bar mu da ƙorafi ko koke-koke a kafafen watsa labarai, muna zagin hukumomi. Tun yanzu mu kula da tsaftace hannaye, rage shiga cinkoso ba tare da takunkumi ba da sauran su, a matsayin rigakafin yaɗuwar cutar Korona.

Kira na ga hukumomin ƙasar nan a tausayawa talaka, a daina fitar da tsare-tsaren da za su ƙuntata masa rayuwa, in dai ba a sassauta masa halin da yake ciki ba.