Sakar wa uwa nauyin ’ya’ya bayan rasuwar mahaifinsu

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Da fatan na same ku lafiya. Yau ma ga mu a filinmu mai albarka, za mu taɓo matsalar da ta addabi mata yanzu. Abinda ya sa na ce ta addabi mata shi ne, yadda matan ke alhini da yadda mazaje suke mutuwa suke barin matansu da nauyin yara, babu mataimaki sai Allah. Ba kuma don ba su da dangin uba ba, suna nan da ransu amma da zarar ɗan’uwansu ya mutu ya bar mace da yaranta, to babu mai damuwa da su, ko taimaka musu. Innallilahi wa inna ilaihi rajiun! Ba wai wannan maganar ƙarya ce ba ko shaci-faɗi ba, yana faruwa, kuma ana tafiya a kan haka. Mata da yawa ana mutuwa ana sa musu ido.

Dangin uba suna manta alhakinsu ne kula da da yaran da ɗan’uwan su ya mutu ya bari, amma ina! Sai kawai su ɗauki ido su sanya mata. Wanda ko a shari’ance, ba dai-dai ba ne, su ne ya kamata su ɗauki ɗawainiya ta yaran ɗan’uwansu ba matar sa ba. Zamani ya zo na rashin zumunci da rowa, da son zuciya, ya sa yanzu ‘yanuwan uba za su bar yaran danuwansu suna walagigi a duniya. Wallahi mu ji tsoron Allah. Shi zumunci in ma ba mu yi a nan ba, to wallahi za mu yi shi a lahira. Babu ta yadda za a yi na ce wai haƙƙin iyalan mamaci ya koma kan uwa. Kuma idan yaran sun girma sun zama wasu, sai dangin uban su zo su fi uwar da ta sha wuyar yaranta tun suna yara. An gaza tallafa musu, amma don rashin gaskiya, kawai sai su ce su ne masu yanke wa yara hukunci.

Da yawa dangi na manta haƙƙinsu na dangantaka, wasu ma ɗan abinda mamaci ya mutu ya bari, sai su handame. Babu tausayi ko imani, babu tunanin yaya rayuwar iyalan mamaci za ta kasance. Kawai hangen su, ‘yar dukiyar da ya bari suke ƙyashin iyalansa su mallaka. Da yawa ba sa bin ƙa’ida da Shari’a ta gindiya. Wanda ba su san bala’in da suka ɗaukar wa kansu ba. Uwar nan dai za a bari da hidimar nema wa yaranta rayuwa. Wasu ana gama zaman makoki suke zare hannayensu daga kan yaran ɗanuwansu. Ba ruwansu da halin da za su shiga, ta yaya zasu ci ko su sha? Yaya batun ilimi, suttura, ciwo, da sauransu? Ba ruwansu ko da kuwa Uwar ta zo nema wa yaran ɗan’uwansu taimako. Don rashin imani ba za su ba da ba. Idan ma ta samu an kula ta, to ta ji da]i. Wasu ma korar kare za su yi mata da baƙaƙen maganganu, ta yadda gobe ma idan an ce ta zo gurinsu, ba za ta zo ba.

Idan Allah ya yi uwar jaruma ce, ita za ta yi faɗi-tashin nema wa yaran ta rayuwa ingantacciya. Da daɗi da babu, haka za ta yi ta sana’o’i ko aiki don kawai ta samu abin rufa wa yaranta da kanta asiri. Amma wani abu na alheri na samun su, za ku ga zugar dangi. Kowa na cewa ‘yarsa ce ko ɗansu ne. saboda kawai don abun duniya. Sun manta irin ɗiban albarkar da suka yi musu a baya, har ma su zaƙalƙale su fi uwar ƙarfi. A nan za a fara yi mata gori da habaici ai ba da su ta zo ba. Sun manta sanda ta zo musu neman abinda za su ci, ko za ta kai su asibiti, ko za ta kai su makaranta. Amma lokaci ɗaya don yaran sun zama wasu, za a nuna wa uwarsu ba ta isa ba.

To me ya sa ne ake nuna halin ko ina kula da yaran ɗan’uwa da ya rasu? Me ya sa ake kasa tallafa musu?  Wasu za su ce babu ce ta jawo haka kuma a ce ai yana da shi. Amma an manta babu ba za ta hana ka yi wa iyalan ƙanuwanka komai ba, saboda suna buƙatar hakan daga gurinku. Amma sai a ƙi taimaka musu. Ana kallo uwa za ta yi ta fafutukar neman yadda za ta yi, babu mai ce mata komai. Yanayi na rayuwa da miji ma yaya mace ta cika balle babu mijin? Yana daga cikin al’adar bahaushe ta ƙin nuna kulawa a kan iyalin mamaci, kuma suna nuna wa matar bambanci kamar ba su santa ba.

Kaɗan ne masu nuna kulawa ko damuwa. Don Allah ta yaya kuwa uwa ko ‘ya’yanta za su girmama dangin ubansu, bayan sun san irin wuyar da suka sha a baya? Dukkan abun da ya dace ka yi wa iyalinka ya kamata ka yi wa ɗan ɗan’uwanka saboda da ma haƙƙinka ne ka yi ɗin. Misali, yanzu macen dake ji da ƙuruciya a mutu a bar ta da yara uku ko huɗu, tana so ta ƙara aure, ana matsalar rashin kulawar dangin uba tasa ta a dole ta haƙura da auren. Dalili babu inda za ta da yara ba tare da mijin da ta aura ya amince ba. Ita kuma ba za ta iya barin yaranta su wulaƙanta ba.Ta kai wa dangin uba sun ce ba za su  iya ba, to yaya ake so ta yi?

Mata da yawa an durƙusar musu da rayuwarsu dalilin ‘ya’ya. Tana ji, tana gani za ta haƙura don ba yadda za ta yi. Idan ma an karɓa, azaba ake gana wa yaran da duka ko da aiki, kuma babu kulawa. Daga nan rayuwar yara ta lalace saboda bautar da suke yi kaman ba mutane ba. Wannan na cikin abubuwan da ke hana wasu iyaye mata aure, sun gwammace su zauna su ba wa yaransu kulawa.

Shi dai kulawa ga iyalan mamatan lada ne kuma da ma sai an yi haƙuri an duba zumuncin, ba wai abinda za a kashe musu ba. Idan kuma har Kun san nauyin nasu ya rataya a kanku, to ku yi ƙoƙarin saukewa. Allah sai ya yi maka sakayya da abunda ka bada ko a nan duniya, ko a can lahira. 

Duk wanda ya kula da Maraya, wallahil ba zai taɓe ba. Wani can ma yi masa kake balle ɗan‘uwanka. Mu ji tsoron Allah, mu sa ikilasi cikin zuciyarmu, sai Allah mu ma ya duba mu.

Idan har an san ba za a kula da iyalansa da ya mutu ya bari ba, to a bar su da abinda ya mutu ya bari, uwarsu ta san yadda za ta yi wa yaranta amfani da shi, ba tare da ta nema gurin wani ba. Amma idan har dangi za su sa wa macen da aka mutu aka bari ido kan abun da mijin ta ya mutu ya bari, akwai matsala. Idan har ba ka da gado a ciki, to ka bar musu abinsu. Amma don rashin gaskiya, sai a taru a yi wa dukiyar magada rub-da-ciki a wawashe, a bar su. Idan sun nemi taimako kuma, a ƙi yi musu wannan rashin imani ne.

Kowa ba ya duba yadda aka tsara kula da rayuwar zumunci a da. A yanzu ba a wannan dubaiyyar, an fi hangen abunda ake da shi, ga wanda ma yake da shi kenan. Wani komai bai ajiye wa iyalinsa ba, amma ana kallo a rasa mai agazawa. Idan yara sun kawo girma sun samu na kansu, sai kuma a ga dangi na tururuwa a matsayi ƙanne uba ko yayye, wanda sanda suke neman tallafawa ba su yi musu ba, sai yanzu.

Ya na da kyau a cire son zuciya a dunƙule a kyautata wa juna, sai a ga komai ya tafi dai-dai.

Abu da muka yi na daidai Allah sa mu dace, wanda muka yi na kuskure, Allah ya maganta mana.

Ma’assalam. Ku biyo mu cikin sati mai zuwa ɗauke da wani sabon jawabin, kar a manta a cigaba da bibbiyar jaridarmu mai farin jini ta ‘Manhaja’.