Tsaron Nijeriya zai inganta a 2022, inji Babban Hafsan Sojojin Ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Juma’a ne shugaban hafsan sojin ƙasan Nijeriya (COAS), Laftanar Janar Farouk Yahaya, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya da cewa, za a inganta tsaro a faɗin ƙasar nan a shekara mai zuwa.

Yahaya ya ba da wannan tabbacin ne a Abuja a wajen rufe taron shekara-shekara na shugaban sojin ƙasa na 2021 mai taken ‘Gina ƙarfin Sojojin Nijeriya wajen yaƙi da barazanar tsaro da ke kunnu kai a ƙasar’.

“A yayin taron, mun tattauna muhimman batutuwan da suka shafi gudanar da ayyukanmu na tsarin mulki da kuma samar da ƙwarewa. Mun kuma yi la’akari da matsalolin tsaro daban-daban da suka addabi al’ummarmu,” inji shugaban sojin.

Ya ƙara da cewa, “saboda haka, abin da muka fi mayar da hankali a cikin shekara mai zuwa zai kasance kan bunƙasa iya aiki don ingantattun ayyuka a faɗin hukumar.”

Shugaban hafsan sojin ya gargaɗi masu ruruta wutar rikici a wurare daban-daban a faɗin ƙasar da su daina ayyukan rashin kishin ƙasa.

Ya ce, sojojin Nijeriya sun duƙufa wajen ganin an dawo da zaman lafiya a kowane ɓangare na ƙasar nan ba da daɗewa ba.

Ya ƙara da cewa, rundunar sojojin za ta ci gaba da bin doka da oda, za kuma ta ci gaba da tabbatar da cewa duk ‘yan ƙasa masu son zaman lafiya sun gudanar da sana’arsu ta halal da kuma gudanar da rayuwarsu ba tare da tsoro ko fargaba ba.

Ya ce, “dole ne mu kai farmaki abokan gaba don murƙushe su da kuma karya su.”

Hukumar ta COAS ta kuma ba da umarnin kafa kwamandojin runduna da su tabbatar da duba tsaftar makamai da harsasai da wuraren ajiye kayayyaki da dai sauransu.

Yahaya ya ce, taron ya baiwa shugabannin sojojin damar tantance ayyukan da suke yi da kuma ƙoƙarin da suke yi na ganin sojojin Nijeriya za su iya tunkarar ayyukan da ke gabansu a 2022 da kuma bayan haka.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da taron shekara-shekara wanda aka fara shi a ranar Litinin, wanda Shugaban hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor ya wakilta.