Zanga-zangar rashin tsaro a Arewa; Abin da ya biyo bayan sako Zainab

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Al’ummomi arewacin Nigeriya sun fara zanga zangar akan rashin tsaron da ke addabar arewacin Nijeriya.

Zanga zangar da aka yi wa lakabi da “A dena Kashemu haka” wato NoMoreBloodShed,

Masu zanga-zangar suna bukatar gwamnatin Nigeriya ta samar da sharo a sassan Nigeriya musamman arewa da a ke wa kisan ƙiyashi

Kuma suna bukatar a tona asirin masu daukar nauyin ƴan ta’adda kowa ya ji,

Suka kara da cewa, idan shugaban ƙasa ba zai iya bada tsaro ga ƙasar ba, to ya sauka ya baiwa wanda ba zai iya.

An dai gudanar da zanga-zangar a jahohin Kano, Zamfara, Sokoto, Bauchi, Kaduna, Niger, da babban birnin tarayya Abuja,

To sai dai kuma, da yammacin ranar juma’a ne jami’an tsaron farin kaya suka gayyaci Zainab Naseer Ahmad wacce i ta ce jagorar zanga-zangar ta jihar Kano.

Sai dai bayan wasu ayoyi sun sako Zainab, inda aka ga sabon rubutu a shafin ta na nuna karaya, wanda shugabanni wannan tafiya suke zargin rubuta mata a ka yi, ba ita bace,

Masu zanga-zangar dai a arewacin ƙasar nan sun tabbatar da cigaban da fitowa yin zanga-zangar a kullum, har sai mahukunta sun saurari buƙatunsu.