Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙungiyar malaman jinya da unguwar zoma a Jihar Katsina sun ba gwamnatin jihar mako biyu su inganta tsaro a asibitoci da ke yankunan da ake fama da matsalar tsaro ko su shiga yajin aiki .
A takardar sanarwar ɗauke da sa hannun sakataren ƙungiyar Idris Bello Idris, ƙungiyar ta nuna takaicin ta yadda ƴan ta’adda suka sace ɗan kungiyar Yusuf Mairuwa a asibitin ƙanƙara kuma har yanzu yana hannun ƴan ta’adda.
Sanarwar ta bayyana cewa ƙungiyar ta ƙasa da reshen ƙungiyar ta jihar da ta ƙaramar hukumar ƙanƙara suna aiki tare su tabbatar da ɗan ƙungiyar da aka sace yana cikin ƙoshin lafiya kuma za su yi iyaka ƙoƙarin su wajen an sako Yusuf Mairuwa.
Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da tsaro a asibitoci da ke jihar tare da ba ya’yan ƙungiyar kariya wajen gudanar da aikin su .
Ta kuma yi godiya ga ya’yan kungiyar bisa irin goyon baya da suke basu a ƙoƙarin da suke yi na kula da lafiya da tsaro na ya’yan ƙungiyar.
A cikin wannan makon ne ƴan ta’adda ɗauke da mayan makami suka kai hari a babban asibitin ƙanƙara inda suka harbi likita tare da sace wasu malaman asibiti biyu.
Yanzu haka likitan na asibiti a garin Katsina yana amsar kulawa bayan rauni da ya samu.