Malami na shirin ɗaukaka ƙara bayan hukuncin kotu na ƙwace kadarorinsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ofishin tsohon Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya ƙudiri aniyar ɗaukaka ƙara akan hukuncin Babbar Kotun Tarayya na ƙwace kadarorin Malami.

Ya ce, Malami bai amince da wasu ɓangarori na gudanar da hukuncin ba don haka zai ɗaukaka ƙara a kai, yana mai umartar tawagar lauyoyinsa da su gaggauta kai lamarin Kotun Ɗaukaka Ƙara.

A cewar Malami yana sa ran Kotun Ɗaukaka Ƙarar za ta yi dogon nazari akan hukuncin da kuma tabbatar da adalci a kai.

A sanarwar da Mohammed Bello Doka, mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai ya fitar, Malami ya kuma yi godiya bisa addu’o’i da fatan alheri daga mutanensa na Jihar Kebbi da ma sauran al’umma a sassan Nijeriya baki ɗaya.

Ya tabbatar musu da cewa hakan ba zai haifar masa da tsaiko ba a ci-gaban harkokin siyasarsa na ganin ya tsayu tuƙuru wajen hidimta musu.

Don haka ne ya yi kira a gare su da su kwantar da hankalinsu tare da kiyaye doka da oda wajen barin kotuna su yi aikin da dokar ƙasa ta tanada.

By Babaji

Leave a Reply