Daga USMAN KAROFI
Ta tabbata Manchester United ta kori Erik ten Hag a matsayin mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United.
An naɗa shi a watan Afrilu na 2022, kuma ya taimaka wa ƙungiyar wajen lashe kofuna biyu na gida, wanda suka haɗa da Carabao Cup a shekarar 2023 da kuma FA Cup a shekarar 2024.
Ƙungiyar ta bayyana godiyarta ga Erik bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake tare da su, tare da yi masa fatan alheri a nan gaba.
Ruud van Nistelrooy zai ja ragamar ƙungiyar a matsayin mai horarwa na riƙon ƙwarya, tare da taimakon tawagar horarwa da ke yanzu yayin da ake neman sabon koci.
Sauran bayanai na zuwa…