Marigayi Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi, OON, OFR

Spread the love

Daga NASIRU WADA KHALIL (PhD)

Na tsakuro wannan bayani ne daga littafin Galadiman Kano Abbas, wanda Aisha Sarki Lamiɗo ta rubuta (an kammala littafin, amma ba a buga shi ba), da littafin Gwarzayen Masarautar Kano na Malam Ibrahim Hussaini Dawakin Tofa (an buga shi a shekarar 2008). 

Sarkin Dawakin Tsakar Gida – (1959 – 1963)

Dan Iyan Kano – (1963 – 1989)

Wamban Kano – (1989 – 2014) 

Galadiman Kano – (2014 – 2025)

Gabatarwa:

Maigirma Galadiman Kano Abbas Sanusi shi ne na biyar a cikin ‘ya ‘ya sittin da hudu da marigayi Sarkin Kano Sir Muhammadu Sanusi (1953-1963) ya haifa. 40 daga cikin su maza ne, kuma 24 mata ne. Yana da yayye kamar haka: Dan Darman Tijjani (Wakilin Yamma) sai Marigayi Wamban Kano Abubakar (Hakimin Bichi) sannan Marigayi Ciroman Kano Aminu Sanusi, da kuma Dan Iyan Kano Ado Sanusi. 

Haka kuma na kasa da shi (Kannensa) sun hada da Mamu da Rufa’I da Haruna da Ibrahim Chigari da Sarki Aliyu da Sayyu da Abdullahi (Lamido) Barden Kano Hakimin Kunbotso da Umaru (Dan Buram Karami) kuma Danburan din Kano na yanzu Hakimin Minjibir. Sauran sun hada da, Nura da Hafizu da Mannir (Galadiman Kano na yanzu) da Isa da Mamhud da Shehu (Makakau) da Akilu da Hafizu da Basiru da Ujudu da Kamilu daYahaya (Abba) da Kasim da Ghali da Abdulaziz (Alhaji) da Mustapha da Yahaya da Mukhtar, Kamilu, Kabiru (Barde) da Idris Sarkin Sullubawa Hakimin Takai da Japar da Abdulkadir (Galadima) da Nasir da Nuhu da Musa da Zubairu da Mu’awiyya.

‘Ya’yan Sarkin Kano Sanusi mata kuwa sun hada da Yalwa (Yalwan Masallaci) da Hauwa (Tafada) da Mairo (Dan Haji) da Aishatu da Zahra ‘u da Halima (Fulanin Ringim) da Sadiya da Hafsatu* da Rabi da Mariya da Yahanasu da Saude da Amina da Sa’adatu da Rakiya da Hasiya da Nafisa da Zainab da Mariya II, da Bilkisu da Ummul Kulsum da Ummuhani da Umul-khairi da Umma Salamat, da Hauwa ‘u II.

Haihuwarsa:

Mai Girma Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi. An haife shi a garin Bichi Shekara ta 1352 Hijiriyya wanda ya yi daidai da shekara ta 1933 Miladiyya, lokacin mahaifinsa marigayi Sir Muhammadu Sanusi yana Hakimin Bichi a matsayin Chiroman Kano. Bayan haihuwarsa da kwana arba’in ne rayuwarsa ta koma gidan marigayi Sarkin Kano Abdullahi Bayero, a lokacin yana Sarautar Kano. Wannan ya faru ne a sakamakon lalurar da mahaifiyarsa ta hadu da ita, ta ciwon nono. Sanadin haka aka yayeshi, aka mai da shi hannun ‘Mai Soran Baki’ ta Sarkin Kano Abdullahi Bayero.  

A lokacin da marigayi Sarkin Kano Abdullahi Bayero ya karbi rainon Mai Girma Galadiman Kano Abbas sai yasa aka nemo saniya Katuwa, lafiyayya, wacce ta ke shayarwa a cikin shanun da ake kiwo na Sarki, domin a ci gaba da shayarda Galadima Abbas da ita. Daga baya aka siyo madarar “NAN” ake bashi wacce a zamanin kwarori ne suke kawowa daga London.

Haka kuma a wannan lokacin dai mai Iura da masu shayarwa (Midwifery) ta kawo robar shayarwa (Feedingbottle) ta bayar domin a rinka shayar da jaririn, kuma ta koyawa iyalan Sarkin Kano Bayero yadda ake amfani da kuma tsaftace wannan kwalba ta shayarda jinjiri.  Wannan ya nuna shi ne mutuum na farko da yayi amfani da feeding bootle a Kano wadda a lokacin ma baki biyu ne da ita sama da kasa ba kamar ta yanzu mai baki daya ba.

Karatunsa:

Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi ya fara karatunsa ne da makarantar Allo, ta koyan karatun Al-ƙur’ani mai tsarki, a makarantar Malam Ali dan Chiroma (A Gidan Sarki Kofar Kudu), wanda marigayi Sarkin Kano Abdullahi Bayero ya saka shi, a lokacin yana da misalin shekaru hudu da haihuwa. 

Bai cika shekaru goma sha biyu da haihuwa ba a ka sa shi a makarantar boko a shekarar 1944, a karkashin kulawar kakansa Alhaji Abdullahi Bayero. Kadan daga daliban da su ka yi karatu tare da Galadima Abbas, a wannan makaranta ta “Elementary” a Kofar Kudu, sun hada da Alfa Wali, tsohon magatakardar Gwamnati Jihar Kano, sai Alkali Sulaiman, da Malam Tanko. Kuma a wancan lokacin ba a bar mata a baya ba. Har a wancen lokacin akwai mata wadanda suka yi karatun “Elementary” ta Kofar Kudu tare da Galadiman Kano. Daga cikin mata da suka yi karatu tare sun hada da Hauwa Sule ‘Yar Ma’aji da kuma Amina (Goggo ta Kori), ita Amina ‘ya ce ga Dan Majen Kano Ahmadu dan Sarkin Kano Alu. Daga malaman da suka koyar da Galadiman a “Elementary” ta Kofar Kudu, akwai Malam Wada, wanda ya yi wakilin Arewa. 

Bayan ya kammala “Elementary School” ne, ya ci gaba da karatunsa a “Middle School”, wacce ake kira, “Rumfa College” a yanzu. Daga abokan karatunsa akwai Rufa’i Ahmad wanda ya taba shugaban, Hukumar Tara Kogunan Hadejia da Jama’are, (Hadejia Jama’are Riɓer Basin Deɓelopment Authority) akwai Alhaji Musa Ringim da Alhaji Aminu Madigro da Ahmad Gumel, da Galadiman Kano Marigayi Alhaji Tijjani Hashim da Malam Imamu Wali da Abdulkadir Chedi da General Sani Abacha da sauransu. Wadannan kadan ne daga mutanen da suka yi karatu tare da shi. Lokacin yana Kwalejin Rumfa malamansa su ka nada shi shugaban dalibai na wannan lokaci a shekara ta 1948. A bangaren Malamai, kadan daga Malaman wannan makaranta a waccan lokacin, akwai Malam Ahrnadu Lura, Malam Muhammadu Mayo, mutumin kasar Adamawa da Alhaji Barau Danbatta. 

A cikin. Shekarar 1950 ne ya samu shiga makarantar koyon Harshen Larabci (School for Arabic Studies). Ita wannan makaranta tana samun dalibanta daga dukkan lardunan da suke kowanne bangare na wannan kasa. Saboda haka karatu a wannan makaranta zai taimakawa dalibai su koyi cudanya da sauran al’ummar wannan kasa. Na kusa-kusa da suka yi karatu tare da mai girma Galadiman Kano Abbas Sanusi a wannan makaranta, akwai Malam Ladan Zariya, wanda ya zo daga lardin Zaria, sai Malam Ahmad Tsiga daga Kebbi ta masarautar Gwandu a lardin Sakkwato, da kuma wasu da yawa wadanda bamu samu damar kawosu ba. 

Bayan Galadiman ya gama makarantar koyon larabci ta S.A.S ne a Kano sai a shekara ta 1954 ya tafi ya karo karatu a Jami’ar Eɗerter a Kasar Ingila. A nan ne ya yi karatun Diploma a fannin siyasa da gudanarwa “Social and Public Admisnirtation”. Abokan karatunsa sun hada da Malam Imamu Galadanci da Marigayi Alhaji Garba Jabo, Bunun Sokoto.

’Ya’yansa:

Allah Ya albarkaci Mai Girma Galadiman Kano Abbas Sanusi da ‘ya’ya 40. Maza 26 mata 14. Jerin sunayen ‘ya ‘yansa” maza su ne kamar haka: Kabiru, Usaini, Abdullahi (Alhaji), Sanusi (Babannani), Aminu (Chiroma), Ibrahim, Ahmad (Dan Darman), Sagir (Yallaboy), Sadiku, Musbahu, Awaisu (Malau), Yusif (Mami), Mu’awiya (ya yi Dan Makwayon Bichi, hakimin Kunci), Muhd Shamsu, Marwana, Tukur (Na’ibi), Arifi, Ka’abul, Usman, Mahmud (Walidi), Muhd Kamaludeen, Abubakar, Ali, da Abbas bin Abbas (Baba). Idan kuma muka koma bangaren mata, akwai Hajiya Kilishi (Amina) Aishatu (Balarabiya) Hadiza (Hajiya), Fatima (Iya), Saratu (Mama), Yahanasu (Maman Agege), Zainab, Kibdiyya, Umma Habiba, Badiatu, Hadiza (Hajiyayye), Hafsatu (Umma), Alawiyya, Maryam.  Sannan ya bar jikoki da yayan jikoki sama da 200.

Aikin gwamnati:

Aiki na farko da Mai Girma Galadiman Kano ya fara shi ne ‘jami’i na kungiyar gama kai” Su wadannan kungiyoyi, yadda ake kiransu da turanci shi ne “Co-operatiɓe Unions”. Mai Girma Galadiman Kano Abbas da wannan ya fara a matsayin sa-na mai kula da Kananan jami’an wannan hukuma wato “Cooperatiɓe Inspector”. Daga nan ne aka ci da shi gaba, aka yi masa: babban jami’i wato “Cooperatiɓe Superɓisor”jami’i mai duba ayyuka na bangaren ‘yan katako. A wannan lokacin aikin katakon wani bakon abu ne a kasar Kano. 

Daga cikin ayyukan da ya yi sun haɗa da:

1. Jami’i mai kula da harkokin kasuwanci a Kano a shekarar 1955-58.

2. Kansilan Lafiya na Kano N.A a shekarar 1965-68

3. Kansilan albarkatun kasa na Kano N.A a shekarar 1968-73

4. Kansilan Kudi a shekarar 1973-76 

5. Shugaban Kwamitin kudi da bayar da kwangiloli a shekarar 1976.

6. Dan kwamitin gudanarwa na Hukumar Gidan Ruwa a shekarar 1976-79

7. Shugaban Mayanka Abattuwa (Manager) ta Kano a shekarar 1974.

8. Dan majalisar gudanarwa ta Hukumar Lafiya ta Jihar Kano 1984 – 1986 

9. Shugaban Kamfanin Sun Insurance Company Ltd.

10. Dan kwamitin gudanarwar Hukumar Kogunan Hadejia/Jama’are.

Wasu daga cikin Ayyukan nan da aka ambata ya yi su ne yana rike da sarauta wasu kuwa tun kafin ya fara sarauta. 

Harkokin siyasa:

A shekarar 1959 ne, Mai Girma Galadimaya fara ayyukan siyasa, lokacin yana Hakimin Ungogo “Sarkin Dawakin Tsakar Gida” a wannan lokacin Sarakuna a matsayin su na iyayen al’umma ba wata doka da ta hana su shiga harkokin siyasa. A cikin wannan shekara ne ta 1959 aka zabi mai girma Galadiman Kano a matsayin dan majalisa ta kasa dake Lagos, mai wakiltar yankunan Kumbotso da Ungogo, a karkashin tutar NPC an sake zaban sa da ya wakilci Kano kafin rushewar gwamnatin. Kadan daga cikin wadanda suka yi aiki tare akwai Solomom Lar da Abdullahi Adamu da Bamanga Tukur da Professor Jibrin Aminu.

Ya riƙe ɗan kwamiti “a majalisar mai kula da asusun alumma mai wakiltar Kano. Haka kuma wakili ne na wadanda suke gudanar da gwamnatin jihar Arewa, a ma’aikatar lafiya ta Kaduna daga nan ne aka sake zabensa a ma’aikatar lafiya, a bangaren hana shan miyagun” kwayoyi (kwayoyi masu sa maye). Haka nan ya rike wakili a sha’anin kudi, a gwamnatin Kano. 

Sarkin Dawakin Tsakar Gida (1959 – 1963):

A shekara ta 1959 aka yiwa mai girma Galadima Abbas sarauta ta farko, wanda marigayi Sir Muhammad Sanusi ya nada shi a matsayin Sarkin Dawakin Tsakar Gida, Hakimin Ungogo. 

Zaman Galadima Abbas Sanusi a Garin Ungoggo:

Ungogo tsohon gari ne wanda ya kafu tun kafin Mulki Fulani, sai dai a lokacin makiyaya ne kanyada Zango a gurin kasancewar da gurin dausayi ne. Garin Ungogo yana da kofofi guda biyar a farkon kafuwarsa.

Hakimin da aka fara turawa wannan yanki na Ungogo shi ne Alhaji Muhammadu Maje Karofi lokacin yana Tafida. An cigaba da kawo hakimai domin gudanar da harkar mulki har ta zo kan Sarkin Dawakin Tsakar Gida Abbas Sanusi a shekara ta 1959 – 1963. Alhaji Abbas shi ne hakimin da ya rike kasar Ungogo na goma sha daya (11), Ga jerin sunayensu kamar haka: 

1. Muhd Maje Karofi – Tafida

2. Yusufu Muhammadu – Tafida

3. Muhammad Shehu – Turaki

4. Muhammadu Inuwa Abbas – Turaki

5. Isa Bayero – Dan Makwayo

6. Umaru Sanda M/Karofi – Dan lsa 

7. Muhammad Umaru – Dan lsa 

8. Alhaji IbrahimAbbas – Dan Lawan

9. Alhaji Abubakar Gidado – Dokaji 

10. Muhammad Dahiru – Makama

11. Sarki Abbas Sanusi – S D/Tsakar Gida

Alhaji Abbas Sanusi ya yi mulki a Ungogo har tsawon shekara biyar.

Ayyukan Ci Gaban Da Ya Samar A Ungogo

-Lokacin da Galadima Abbas ya je garin Ungogo makaranta daya ce a wannan yanki wato “Central Primary School.” ita ma babu wadatattun ajujuwa, haka kuma lokacin zamansa ne a garin aka gina;

i. Kadawa Primary School.

ii. Rangaza Primary School.

iii. Zangon Gabas Primary School.

-A lokacin sa aka gina rijiyoyi da dama a garin yankin Ungogo, daga ciki akwai Rangazan Gabas, Bela, Rijiyar Zaki da Kurnar Asabe, a lokacin suna cikin yankin Karamar Hukumar Ungogo. 

-A lokacinsa ne jama’ar yankin Ungogo suka zage dantsen cinikin fata da kirgi domin a lokacin Alasawa su ka fara shiga garin domin sayen fata da kirgi. 

-A lokacinsa ya kyautatawa masu tafsirul Jalalaini don su ji dadin fadakar da jama’ ar yankin.

-AI’umar Ungogo sun ce Galadima yakan kira jama’ar yankin gonarsa idan zai zuba takin zamani don su san muhimmancin takin.

-Akan harkar makaranta yakan kira taron bita ga malamai don kara musu karfin guiwa dajawo jama’a su sami amfanin ilimi hakan ce tasa har yakan je ajujuwa don koyawa yara ko tambayar yara wanda ya bayar da amsa ya yi masa kyauta ta musamman.

Dan Iyan Kano:

A cikin shekara ta 1963 Sarkin Kano Inuwa ya yi wa Mai Girma Galadima sarautar Dan Iya, hakimin Kiru, wanda ya zauna tsawon shekara uku zuwa hudu daga nan sai aka dauke shi daga Kiru aka mayar dashi Gundumar Waje, a inda ya rike Sabon Gari, Gwagwarwa da kuma Bompai, nan ya yi shekara daya da rabi. Daga nan sai aka daukeshi aka mayar da shi gundumar Nassarawa a shekara 1972 a lokacin Nassarawa Sabuwar kirkira ce. Daga Nassarawa ne aka sake Mayar da shi Kasar Kiru, ya zauna kimanin shekara guda. Sai aka sake mayar dashi kasar Nassarawa, a nan ne bai dadeba aka yi masa karin girma ya zama Dan Majalisar Sarki (Councillor).

Wamban Kano, Babban ɗan Majalisar Sarki:

A shekarar 1984 yana Dan Iyan Kano aka kara masa girma zuwa babban dan majalisar Sarki (Senior Councillor). Bayan nan ne a shekara ta 1989, bayan mutuwar Mai Girma marigayi Wamban Kano Mahmud Usman Ringim, Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya bashi sarautar Wambai. 

Galadiman Kano:

A Shekara ta 2014 ne Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya baiwa Maigirma Wambai Abbas sarautar Galadiman Kano, bayan rasuwar marigayi Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (1992 – 2014). An nadashi wannan sarauta ne a ranar Juma’a 10 ga watan October, 2014. Shi ne mutum na 44 da ya rike wannan babbar Sarauta ta Galadima tun daga fara yinta a Kano lokacin Habe, a jerin wadanda suka rike Sarautar daga Zamanin Fulani shi ne na 22. 

Dama wani abin sha’awa shi Galadiman Kano Abbas ya yi zamani da sarakuna guda hudu kowanne sarki ya yi masa nadi sau daya, Sarkin Kano Muhammdu Sanusi I ya fara nada shi Sarkin Dawakin Tsakar Gida, Sarkin Kano Inuwa ya nadashi Dan Iya, Sarkin Kano Ado ya nadashi Wambai sai Muhammadu Sanusi II ya nadashi Galadima.

Lambar yabo ta ƙasa:

Tun a shekarar 2002 Gwamnatin Tarayyar Nigeria ta yaba da irin ayyukan da Galadima ya ke yi ta bashi lambar Girma ta OON bayan shekara guda sai ta bashi lambar girma ta OFR a shekara ta 2003.

Kirarin da Wasu Masarautan Kano suke yi Masa:

Hasken Fadar Kano yana yi masa kirari da cewa;

-Dabaibayi mai tsare Shanu

-Ruwan da Kada, kowa ya shiga ya hadiye shi

-Babbar duhuwa mai karar da itace.

Waƙoƙin da aka yi masa:

Sarkin Taushin Kano Bala Makaɗa

Haka kuma Sarkin Taushin Kano Bala Makada ya ce: “Gagarau dan Muhammadu, Wambai ka fi ƙarfin magautan Giwa.” 

Sani Aliyu Dandawo:

Kamar yadda Sani Aliyu Dandawo shi kuma ya ce: “Abbas Sanusi ɗan Gogarma karo da kai maza ke shakka”.

Maje Ahmad Gwangwazo:

Shi kuma shahararren marubucin tarihin Kano, Alhaji Maje Ahmad Gwangwazo, ya bayyana ƙwarewa da halayyar Galadiman Kano a lokacin yana Wamban Kano, ya yi wannan bayanin ne a cikin littafinsa mai suna “Kano da Sarakunanta” inda yake cewa:

“Jama’a suna gaishe ka tare da addu’a, 

Wamban Kano marikin amanar San Kano.

Kullum idan Sarkin Kano ba ya gari,

Kai ne wakili mafawwalin Sarkin Kano.

In dai batun mulki ake ba gardama,

In dai su Wambai sun iso Fadar Kano.

Shi ne Abbas goyon gidan Sarkin Kano.

Jika ga Bayero Adalin Sarkin Kano

Allah ya yi masa baiwa a harkar sarauta mai tarin yawa kuma yana alfahari da su:

-Shi ne Babban ɗan Majalisar Sarki da ya fi kowa daɗewa yana riƙe da wannan babbar kujera a tarihin masarautar Kano,

-Shi ne hakimin tilo da yake cikin majalisar sarakuna ake zama dashi bayan sarkinsa.

-Shi ne wanda yana hakimi a Kano Dansa yana hakimi, wannan ma ba a taba samu ba.

Taimakon addininsa:

Kasancewar wannan dan gajeren rubutun na Marsiyya ne shi yasa zan waiwayi irin kokarin da Galadiman kano Abbas ya yi na bunkasa addinin Musulunci, ta assasa makarantu, gina Masallatai da taimakawa shugabannin addini. Daga cikin irin masallacin daya gina shi ne na gidan Sarautar Kiru lokacin yana hakimci a garin. A kasar Ungogo kuma shi ya fara futo da tsarin taimakawa masu Tafsiril Jalalaini a yankin, baya ga makarantun boko da na Islamiyya da ya samar a garin na Ungogo. 

Da wannan ne nake rufewa tare da adduar samun dacewa da rahmar Ubangiji a rayuwarsa ta Barzahu.
Za a iya tuntuɓar Nasiru Wada Khalil (PhD) a imel ɗinsa kamar haka; [email protected]

By ukarofi