Masarautar Bauchi ta buƙaci gwamnati ta zaƙulo tsagerun da suka kai wa Sarki farmaki

Daga BAKURA M. MUHAMMAD a Bauchi

Majalisar Mai Martaba Sarkin Bauchi ta yi tir da abin da ta kira rashin mutunci, tsokana da haɗa ruɗani, ta’asar da ta auku ranar satin da ya gabata da wasu tsageru suka yi wa tawagar Sarki Alhaji Rilwanu Suleiman da takwaran sa na garin Dass, Alhaji Usman Bilyaminu Othman harin ta’addanci, lalata motocin su da tilasta masu komawa gida daga kan hanyar su ta zuwa wani taro a garin Bogoro, domin gujewa hasarar rayuka da dukiyoyi.

Majalisar masarautar, a sakamakon wani taron gaggawa da ta yi a ranar Talata danta gabata, ta yi kira ga gwamnatin jiha da ta gaggauta kafa wani kwamiti mai kima da zai binciko dalilan da suka sanya ‘yan tsagerun suka aikata wancan aika-aika wa shugabanni, domin yi masu hukunce-hukuncen da suka dace da laifukan su.

Galadiman Bauchi, ma’abucin ilimin safiyo Ibrahim Sa’idu Jahun, wanda ya yi jawabi wa manema labarai a madadin majalisar, ya ce “majalisa ta kuma buƙaci gwamnatin jiha ta roƙi Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani bincike daban akan lamarin da zummar ganin irin hakan bai sake faruwa a kowane sashi na ƙasar nan ba.”

Alhaji Ibrahim Jahun ya kuma bayyana cewar, abin takaici ne a wannan zamani da lamuran tsaro suka zame gagara-badau a jiha da ƙasa baki ɗaya, a ce an samu wasu marasa kishi suna tayar da hankulan jama’a a birane da ƙauyuka.

Ya kuma yi matuƙar mamakin farmaki da ‘yan tsagerun suka kai wa sarakunan akan hanyar su ta zuwa Bogoro domin amsa gayyata da aka yi masu na bikin tunawa da wani gwarzon namji, Marigari Peter Gonto, da ya mutu yana fafutukar nemawa al’ummar sa ta Sayawa ‘yanci, kuma bisa wannan aniyar sarakunan ne wasu ‘yan tsageru suka yi wa tawagar sarakunan tsinke akan hanya, tare da lalata masu motoci a cikin tawagar.

A kuma halin da ake ciki, al’ummar Sayawa suna bai wa gwamnatin jiha tabbacin haɗin kai bisa ko waɗanne irin matakai za ta ɗauka domin zaƙulo waɗanda suka aikata tashin-tashinar ta ranar Asabar da ta gabata, waɗanda suka yi farmaki wa tawagar sarakunan Bauchi da Dass.

Al’ummar ta Sayawa sun nuna nadamar su ga Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed, Sarakunan Bauchi da Dass. Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu da Alhaji Usman Bilyaminu Othman, da Mawaƙi Dokta Panam Percy Paul, da ɗaukacin al’ummar jiha bisa faruwar lamarin, musamman waɗanda aka lalata masu motoci, kayayyakin kaɗe-kaɗe da dukiyoyi a lokacin hargitsin na wancan Asabar.

Sarakunan biyu dai, idan ba a mance ba, suna kan hanyar sune zuwa garin Bogoro wajen bikin tunawa da Gwarzo Peter Gonto wanda ya rasu kimanin shekaru 21 da suka shuɗe, da aka ayyana yin bikin a ranakun 30 da 31 na watan da ya gabata, yayin da wasu tsageru suka kaiwa tawagar sarakunan farmaki bisa nuna rashin amincewar su na yin bikin.

Wakilan al’ummar ta Sayawa ƙarƙashin tutar wata ƙungiya ta Bunƙasa Al’adun Gargajiya, a wani taro da suka yi da manema labarai a garin Bauchi, sun aibunta faruwar lamarin, da suka ce ya rage kimar Sayawa a idanun jama’a.

Shugaban Ƙungiyar Bunƙasa Gargajiya ta Sayawa, Injiniya Isuwa Galla ya nuna nadamar faruwar lamarin a madadin al’ummar Zaar, har ma da waɗanda suke ƙasashen ƙetare, tare da nuna buƙatar hukumomin tsaro na cikin jiha su tuhumi tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Rt. Hon. Yakubu Dogara dalilan sa na cewar, matuƙar aka raja’a kan gudanar da taron, zai haifar da tashin-tashina a yankin na al’ummar Sayawa.

“Dogara ya kuma yi shaguɓe a cikin wata takarda da ya rubuta wa Babban Sufeton ‘yan sanda na ƙasa, wacce kuma kofen ta aka watsa a yanar intanet inda yake cewar, gudanar da taron ba zai haifar da alheri ba, kuma waɗanda suka shirya taron basu da hurumin yin hakan, kuma basu da albarkacin iyalan Marigayi Gonto, ko ɗaukacin jama’ar mahaifar marigayin, wato ƙauyen Mwari na shirya wancan taro wanda daga bisani aka samu akasin yin sa.

“Harwa yau, a ranar 25 ga watan Disamba ne, ko kwatankwacin hakan, Rt. Hon. Yakubu Dogara a wani saƙon rubutu da ya jefa a shafinsa na Facebook ya yi ƙoƙarin kare aniyar sa na ganin cewar, taron bai yi tasiri ba,” inji Galla.

‘Ya’yan marigayi Baba Peter Gonto, waɗanda ya bari a raye, a ranar 27 ga watan Disamba, 2021 sun rubuta wasiƙa ga Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed wacce a jefa kofen ta a cikin yanar intanet, wacce kuma a cikin ta suke nuna amincewa da yardar su na gudanar da taron da aka sanya a gaba, tare da haɗin kan Ƙungiyar Bunƙasa Al’adun Sayawa ta ZDA da wasu masu ruwa da tsaki a cikin ƙaramar hukumar ta Bogoro, da zummar cimma nasarar gudanar da taron.

A gefe guda kuma, a gabanin gudanar da taron na tunawa da Gonto, shugabannin ƙananan hukumomin Bogoro da Tafawa Ɓalewa, inda al’ummar Sayawa ta yi tunga, a matsayin su na manyan jami’an tsaro na majalisosin su, sun rubuta takarda wa Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar Bauchi, inda a ciki suka bayyana cewar, bisa rahotannni da suke samu daga sassa daban-daban na yankunan su, babu wata barazanar tsaro ga taron da aka shirya gudanarwa.

Kwamitin da aka kafa na shirye-shiryen gudanar da taron, da haɗin kan iyalan Marigayi Gonto sun amince a gudanar da bikin tunawa da marigayin a ranakun 30 da 31 ga watan Disamba da ya gabata, haɗi da ƙaddamar da wani littafi da gidauniyar tuna marigayin, Baba Peter Gonto, wanda suka yi wa laƙabin ‘Gwarzo’ kuma ‘Jigo’ na al’ummar Sayawa, amma kash, sai wasu tsageru suka yi ta yaɗa jita-jitar cewa, za a yi bikin ne domin naɗa Sarkin al’ummar Sayawa, wato ‘Gung Zaar’ a Bogoro, da kuma naɗa tsohon gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Ahmad Adamu Mu’azu a matsayin Sarki a garin Tafawa Ɓalewa.

Idan ba a mance ba dai, Baba Peter Gonto ya rasu ne a shekara ta 2000, kuma tun wancan lokaci, babu wata qungiya, hukuma ko ɗaiɗaikun jama’a da suka yi ko ya yi tunanin tunawa da marigayin, sai wannan shekara ta 2021 da ta shuɗe, da iyalan sa da haɗin kan ƙungiyar gargajiya ta ZDA da wasu masu ruwa da tsaki suka ga ya dace a yi bikin tunawa da shi a ƙauyen su, bikin da gudanar da shi ya cimma tura sakamakon katoɓarar wasu tsagerun mutane.

Jigo, Marigayi Baba Peter Gonto Mwari (1882 -2000) an haife shi a ƙauyen Mwari, inda ya tafiyar da rayuwar sa, ya rasu shekaru 21 da suka gabata, kuma kushewar sa tana nan har yanzu a ƙauyen Mwari da ke cikin ƙaramar hukumar Bogoro. Ya yi rayuwa abar koyi, nitsattse, kuma jagoran fafutukar nema wa sayawa ‘yanci. Ya yi rayuwa mai ban sha’awa na tafiya kafaɗa-da-kafaɗa da jama’ar sa ta Sayawa, har ma da maƙwabtan su.
Shugaban Ƙungiyar Al’adun Sayawa, Isuwa Galla da manema labarai suka yi masa tambaya ko an rasa rayuka a cikin rikicin, sai ya amsa da cewar, haƙiƙa an rasa rayuka, amma bai san yawan su ba, yana mai takaicin wasu ‘yan baranda sun haddasa gaba a tsakanin Sayawa su-ya-su, ya kuma buƙaci hukumomin tsaro da kada su sake wannan lamari ya tafi a iska.

Ita dai rundunar ‘yan sanda ta jiha, a cikin rahoton da ta rabawa manema labarai bayan da rikicin ya lafa, ta shaidar cewa, an ƙona gidaje kimanin guda goma yayin rikicin da ya tashi a cikin al’ummar Sayawa, a ranar da za a gudanar da bikin na tunawa da Marigayi Gonto, yayin da motoci da ɗimbin dukiyar jama’a na miliyoyin nairori suka salwanta.

A wani jawabi da jami’in ‘yan sanda mai hulɗa da jama’a, Sufuritanda Ahmad Mohammed Wakil ya gabatar, ya zayyana sunayen mutanen da aka ƙona masu gidaje, da suka haɗa da Mista Peter Roko, Injiniya Isuwa Galla, Mista Kura Sang KK, Sarkin Yaƙi Amos, Mista Habila Samu Sur, Mista William Wotni, Mista Mamaki Ishaya, Sarkin Bogoro Nuhu tafida, Mista Luka Maiciki, da Mista Gashon Godiya.

Sufuritandan ‘Yan Sanda Ahmed Wakil ya bayyana cewar, katovarar ta tsagerun da ta haɗa maza da mata ta haɗa da farmaki akan jama’ar da ba su ji ba, balle gani, ƙone-ƙonen gidaje, da kuma yin tunga akan manya-manyan hanyoyin safara da zummar wulaqanta jama’a, hatta katafaren filin da aka shirya yin taron, wanda aka daje da kayayyakin ƙawa na gudanar da biki, kayayyakin kaɗe-kaɗe, sun sha wuta.