Saraki ya jajenta kashe al’umma a Zamfara

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

“Cikin jimami nake miƙa ta’aziyyata ga iyalai da al’umman da suka rasa masoya da dukiyarsu.

“Yayin da muke jimamin mummunan farmakin da aka kai a ƙananan hukomomin Anka da Bukkuyum dake Jihar Zamfara, dole ne mu ƙarfafi zukatan mutanen wannan yanki da ma na sauran yankunan da ke fama da rashin tsaro a faɗin Nijeriya. Mu kuma yi musu albishir da samun rayuwa cikin aminci.

“A watan Janairun 2013, lokacin da aka samu ɓarkewar annobar guba a Bagega, na samu zama da mutanen Ƙaramar Hukumar Anka ta Jihar Zamfara. A wannan zaman na fahimci mutane ne jajirtattu waɗanda ke da tsarin kasuwanci mai ƙarfi.

“A yau, wannan yanki wanda mutanensa ke da zimma, suna cikin tashin hankali na mamaya daga ‘yan bindiga. Zuciyata ta zafafa, tsakani da Allah ba zai yiwu mu ci gaba da tafiya a haka ba. Dole ne a nemo mafita ga wannan matsalar tsaro; kuma za mu samar da mafitar da yardar Allah.”

Tsohon Shugaban majalisar dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya jajanta kisan gillar da aka yi a wasu ƙananan hukomomin Jihar Zamfara.

A jiya ne dai ‘yan bindiga suka kashe mutum sama da 200 a ƙananan hukomomin Anka da Bukkuyum da ke Jihar Zamfara. 

Bukola Saraki wanda tsohon gwamnan Kwara ne ya yi wannan jaje ne a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce, zuciyarsa na cikin radadi da damuwa.

Ga cikakken saƙon nasa:
“Na yi imanin cewa, waɗannan mutane za su samu ingantacciyar rayuwa, domin ni shaida ne ga jajircewa irin ta mutanen Anka, Bukkuyum da garuruwa makamantansu.

“Addu’ata ita ce, idan aka samar da shugabanci nagari, kuma da tsaro, wurare kamar Anka su kasance cibiyoyin samar da Kuɗaden shiga ga Nijeriya. Sai dai, kafin a iya cimma wannan, dole ne mu ɗauki matakin da ya dace, mu yi abin da ya dace don kare rayuka da dukiyar dukkan ‘yan Nijeriya,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *