Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
Masarautar Kabin Argungu da ke Jihar Kebbi ta warware rawanin sarautar Maifulanin Kabi Alhaji Usman Muhammed Bakaramba.
Wannan yana ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da sa hannun Alhaji Lauwali Labbo Argungu, sakataren majalisar masarautar da aka rabawa manema labarai ranar Litinin ɗin da ta gabata.
Takardar ta bayyana cewa warware rawanin sarautar Maifulanin Kabi Alhaji Usman Muhammed Bakaramba ya biyo bayan samun sa da aka yi da hannu dumu-dumu a cikin harkokin ta’addaci da hukumar ‘yan sanda ta bankaɗo.
Har wa yau takardar ta gargaɗi tuɓaɓɓen basaraken da kada ya sake danganta kansa da masarautar ta kowane hali, haka-zalika masarautar kuma ta ja hankalin al’umma musamman fulani da kada su sake ƙulla wata alaƙa da ta shafi masarautar da shi.