
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
‘Yan aikin haƙar ma’adinai guda bakwai sun rasa rayukansu bayan ƙasa ta haɗe da su a ƙauyen Kassa da ke Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato.
Wani ɗan yankin mai suna Albert Ɗanlami ya shaida wa manema labarai cewa masu aikin sun haɗu da ajalinsu ne bayan da ƙasar wajen ta rufta akansu, lamarin da ya sa mazauna da sauran abokan aikinsu suka gaggauta yunƙurin ceto su.
Ya ce, al’amarin ya haifar da firgici a ƙauyen yayin da mazauna suka gaggauta zuwa yankin domin bayar da agajin gaggawa kan al’amarin, inda a sanadiyyar haka wasu suka jikkata sakamakon rauni da suka samu.
Sakataren yaɗa labaran Ƙungiyar Matasan ƙabilar Berom, Rwang Tengwong ya tabbatar da rashin, inda ya ce masu haƙar ma’adinai bakwai ne suka rasu a sakamakon faruwar iftila’in.
Wannan al’amari ya sabunta damuwa kan halin lafiya da tsaro a wuraren aikin haƙar ma’adinai a sassan Jihar Filato, inda gudanar da harkokin ba bisa ƙa’ida ba ya zama ruwan dare.
A ranar 19 ga watan Fabarairu ne wani abin fashewa a wurin haƙar ma’adinai a yankin Kampani Zurak da ke Ƙaramar Hukumar Wase ta jihar ya halaka kimanin mutane 33, a cewar gwamnatin Filato. Daga bisani Shugaban ƙaramar hukumar, Hamisu Anani ya ce waɗanda suka rasu sun kai mutum 37 yayin da aka garzaya da wasu 25 sakamakon jikkata a yayin al’amarin.
Daga bisani Ministan Ci-gaban Albarkatun Ƙasa, Dele Alake ya umarci a rufe wuraren da abin ya shafa da Mining Licence 11810 ya ba lasisi, wanda kamfanin Soli Unit Nigeria Limited yake gudanarwa.
