Masu larurar laka sun amfana da tallafin Gwamnatin Kano

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da tallafin kayayyakin kula da kiwon lafiya ga masu larurar laka a jihar da kuɗinsu ya tasamma sama da Naira miliyan bakwai tare da ba su tallafin kuɗi na Naira miliyan ɗaya don gudanar da bikin zagayowar ranar masu larurar laka ta duniya.

Kwamishinar Ma’aikatar Mata, Ƙananan yara da masu buƙata ta musamman, Hajiya Aisha Lawan Saji Rano ce ta bayar da kayayyakin ga Kungiyar Masu Larurar laka a shalkwatar ma’aikatar da yammacin wannan rana.

Kayayyakin da aka bayar sun haɗa da; keken zama (Wheel chair) guda 20, audugar mata, man tsabtace hannu, katata, bandeji da kayan dressing, da dai sauran su.

Bayan kammala taron ne wakilinmu ya zanta da kwamishinar akan yadda aka gudanar da rabon kayan inda ta bayyana cewa, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sahale wa ma’aikatar ne domin mata, kananan yara da masu buƙata ta musamman su ma su san gwamnatin jihar ta na damawa da su.

Ta ƙara cewa, mutane da dama musamman masu buƙata ta musamman da masu larurar laka suna zuwa ma’aikatar suna kai kokensu na rashin irin waɗannan kayayyakin amfanin yau da kullum.

Don haka gwamnan ya bayar da umarnin a samar musu da abinda ya sawwaka don a rage musu raɗaɗin damuwar su.

A nasu bangaren, wasu daga cikin mutanen da suka amfana da tallafin musamman shugabancin kungiyar masu bukata ta ɓangaren masu larurar laka, sun bayyana jin daɗinsu sakamakon yadda suka ce sun daɗe su na neman mai share musu hawaye akan damuwar su tare da neman waɗannan kayayyakin amma ba su da kuɗin saya.

A karshe, sun ce nan da 1 ga watan Disamba za su gudanar da bikin zagayowar ranar masu larurar laka wanda Majalisar Ɗinkin Duniya take warewa, sannan su bai wa mambobin ƙungiyar musamman waɗanda ke da buƙata.

By Babaji