Mata 800,000 na rayuwa da cutar yoyon fitsari a Nijeriya – Rahoto

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Asusun kula da yawan jama’a na Majalisar Ɗinkin Duniya UNFPA ya bayyana cewa akwai mata fiye da dubu 800 da ke rayuwa da cutar yoyon fitsari a sassan Nijeriya da kaso mai yawa a Arewacin ƙasar.

Shugaban ofishin na UNFPA reshen jihar Adamawa Dr Danladi Idrissa a jawabinsa yayin yaye mata 50 da suka warke daga cutar ta yoyon fitsari ya ce fiye da rabin masu kamuwa da wannan lalurar ta yoyon fitsari na Arewacin ƙasar wanda ke da nasaba da al’adun al’ummar yankin.

Dr Idrissa ya bayyana cewa mata 225 cikin 265 da aka yi wa aikin yoyon fitsari sun warke garau ƙarƙashin jagorancin asusun na UNFPA da gidauniyar Fistula da kuma haɗin gwiwar ma’aikatar kula da harkokin mata a Nijeriyar.

A cewar ƙwararren likita akwai mata 40 da ke buƙatar tiyata ta musamman waɗanda rashin kayan aiki a jihar Adamawa ya hana iya aiwatar da tasu tiyatar.

Masana kiwon lafiya na alaƙanta cutar ta yoyon fitsari ga mata da auren wuri baya ga doguwar naƙuda a gida, dalilan da ake ganin su ne kan gaba wajen haddasa lalurar.