Matar da ta fi kowa tsufa a duniya, Itooka Tomiko, ta mutu

Spread the love

Matar da ta fi kowa tsufa a duniya ’yar asalin ƙasar Japan mai suna Tomiko Itooka ta mutu ta na da shekaru 116. 

Hukumomi a birnin Ashiya da Tomiko Itooka ke zaune ne suka sanar da mutuwarta tana da shekaru 116.

Itooka tana da yara 4 da jikoki guda 5, tana rayuwa a gidan kula da lafiya na tsofaffi kuma ta mutu a ranar 29 ga watan disambar bara.

Ta koma rayuwa a gidan ne tun shekarar 2019. An haifeta a ranar 23 ga watan Mayu na 1908 a Osaka kusa da Ashiya.

A shekarar 2024 ne aka amince da Itooka a matsayin wadda ta fi kowa daɗewa a duniya bayan mutuwar wadda ta gada ’yar ƙasar Sifaniya Maria Branyas morera mai shekara 117.

Itooka ta yi tsawon rayuwa kuma taga abubuwa da yawa da suka haɗa da yaƙin duniya da annoba da kuma fitowar fasahohi daban-daban a doran duniya.

By ukarofi