
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Matasa a ƙasar Kenya sun yi watsi da hukuncin Shugaban ƙasar, William Ruto na korar da dama daga cikin manyan ma’aikatansa inda suka ce za su yi zanga-zangar neman ya yi murabus daga muƙaminsa matuƙar bai janye daga batun aiwatar da hakan ba.
Shugaba Ruto ya yi ta ƙoƙarin dakatar da fitina a ƙasarsa inda a kwanakin baya ne aka shirya wani zanga-zanga na ƙin amincewa da hauhawar kuɗin haraji inda hakan ya rikiɗe zuwa tashin-tashina da ya faɗaɗa zuwa ƙiyayya ga gwamnatin.
Zanga-zangar wacce aka shirya ta kafar sadarwa da wasu taron matasa ƴan ‘Gen-Z Kenyans’ suka jagoranta ya haifar da jefa gwamnatin Ruto cikin mawuyacin hali wanda hakan ya tilasta shugaban janye ƙudirin da ya sabbaba hauhawar kuɗin harajin.
A wani yunƙuri na kawar da zaman ɗar-ɗar a ƙasar, Ruto ya sallami duka ministocinsa har da Antoni Janar, illa mataimakinsa da kuma ministan harkokin ƙasashen waje wanda hakan bai yi wa fusatattun matasan daɗi ba, saboda Ruto bai cika alƙawarin da ya yi musu ba na samar da ayyukan yi da kuma inganta rayukansu a lokacin zaɓe.
