Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An kama wani matashi mai shekaru 24, mai suna Usman Mohammed Iyal bisa zargin yi wa ‘yar shekara 16 fyade da yunƙurin halaka ta ta hanyar jefa ta a cikin rijiya a cikin birnin Katsina.
Manhaja ta rawaito cewa an daƙile yunƙurin wanda ake zargin ne a yayin da ‘yan sanda suka ɗauki matakin gaggawa na bincike wanda ya kai ga ceto yarinyar daga rijiya.
Lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Satumba a yayin da mahaifiyarta ta aike ta.
A cewar rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, wanda ake zargin da ke ɗauke da wuƙa ya yi wa yarinyar barazana tare da kai ta wani kango inda ya yi mata fyaɗe.
A wani yunƙuri na ɓoye laifinsa, wanda ake zargin ya jefa yarinyar cikin rijiya bisa niyyar kashe ta.
Mahaifin yarinyar, Abdullahi Sabitu, ne ya kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda.
‘Yan sanda sun yi nasarar ceto yarinyar daga rijiyar tare da kama wanda ake zargin.
Yarinyar dai na ci gaba da karɓar kulawar likitoci a yayin da ake ci gaba da bincike.
