Matashiya ta maka likitar da ta bari aka haife ta a kotu

Wata matashiya da ta yi ƙarar likitar mahaifiyarta a kotu, saboda ta bari an haife ta, za ta samu miliyoyi a matsayin diyya.

Evie Tombes ta yi ƙarar likitar mahaifiyarta ne kan kuskure yayin ɗaukar cikinta da maharfiyarta ta yi, inda ta bari aka haife ta da wata cuta da ake kira ‘Spina Bifida’ a shekarar 2001.

Cutar da ba a cika samun ta ba ta na shafar ƙashin baya ne kuma wasu lokutan ta na nakasa mutum har abada. Hakan ya sa Evie a duk rayuwarta sai an jona ma ta robobi na magani.

Evie za ta samu matsaloli na motsawa a nan gaba, inda hakan na nufin za ta shafe mafi yawan rayuwarta ne a kujerar guragu, sannan za ta samu matsalar bayan gida da ƙoda.

Matashiyar mai shekaru 20, wacce ta ke fafatawa a wasan tsallen doki da mutane masu nakasa har ma da masu lafiya su ke yi, ta yi iƙirarin cewa, likita Dakta Philips ba ta faɗa wa mahaifyarta ta riƙa shan sinadarai masu gina jiki ba kafin ta ɗauki cikinta.

Mai Shari’a Rosalin Coe QC ta goyi bayan Evie a yayin yanke hukunci a wata Babban Kotun Landan a ranar Larabar makon jiya. Alƙalin ta ce, da an ba wa mahaifiyar Evie shawarwarin da suka dace, da ta jinkirta ɗaukar cikin.

Lauyoyin Evie sun ce, a yanzu ba a gama lissafa adadin kuɗin diyyar da za a biya ta ba, amma sun ce kuɗi mai yawa ne domin tana buqatar kuɗaɗen da za ta kula da lafiyarta.

Evie ta gana da ’yan gidan sarautan Ingila, Yarima Harry da Megan Markle a shekarar 2018 a lokacin da ta lashe wata kyauta ta yara a taro da Well Child ta shirya.

Tunda farko, budurwar mai suna Evie Toombes, mai cutar Spina Bifida, ta kai ƙarar Likitarta da gazawa wajen kula da mahaifiyarta lokacin da ta ke ɗauke da cikinta shekaru 20 da suka gabata.

A cewarta, Likitar ta ƙi bai wa mahaifiyarta shawara ta sha wasu magunguna da ka iya kawar da cutar lokacin da ta ke cikin mahaifa.

Mahaifar mai suna Caroline, mai shekaru 50 yanzu ta ce, lokacin da ta tuntuɓi Likitar a 2001 kuma suka yi magana kan Folic Acid, bata faɗa ma ta shan maganin zai hana jaririyarta kamuwa da cutar ‘Spina bifida’ ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *