Ta banka wa budurwar mijinta wuta har lahira

Daga WAKILINMU

Wata matar aure mai ’ya’ya uku a jihar Ogun, Kehinde, ta yi wa budurwar mijinta wanka da man fetur sannan ta cinna ma ta wuta kuma hakan ya yi sanadiyar mutuwarta.

Kakakin hukumar ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ta tabbatar da labarin inda ta ce, tuni an damƙe matar.

A cewar ’yar sandan, sun damƙe matar ne bayan tsohon mijin matar da aka ƙona mai suna Fatai Olugbade ya kai ƙara hedikwatarsu da ke Ota. Fatai ya bayyana wa ’yan sanda cewa, tuni sun rabu kuma ta koma soyayya da wani.

Ya ce, “ina zargin tana hulɗa da wani kwarto mai suna Ismail Wasiu, sai na tambayeta gaskiyar lamarin, amma abin mamaki shi ne ta kwashe kayanta ta koma gidan kwarton.”

Ya ƙara da cewa, “a ranar 14 ga Nuwamba, sai rikici ya ɓarke tsakaninta da matar Wasiu, kawai sai matar ta yi mata wanka da Fetur ta cinna ma ta wuta.”

“’Yan uwanta sun garzaya da ita asibiti amma ta mutu daga baya,” inji shi.

Kakakin ’yan sandan ta bayyana cewa, tuni suka fara neman matar Wasiu kuma suka damƙe ta.

“Yayin bincike, ta amsa laifin amma ta ce, ba ta san abin da ya kai ta ga aikata haka ba,” inji kakakin ’yan sandan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *