Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana wasu sababbin bayanai da suka shafi ƙalubalen da matatun man Nijeriya ke fuskanta, ciki har da yunƙurin mayar da matatun zuwa wani kamfani da bai yi nasara ba da kuma asarar kuɗaɗe da aka yi a ƙarƙashin gwamnati.
A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da gidan talabijin na Channels Tɓ, wanda Wakilinmu ya sa ido a ranar Alhamis, Obasanjo ya tattauna batun matatun mai na Fatakwal, Warri da Kaduna, inda ya jaddada ƙoƙarinsa na neman taimako daga waje domin gyara su da kuma kula da su a lokacin mulkinsa.
Ya bayyana yadda Kamfanin Shell, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin mai a duniya, ya ƙi ɗaukar nauyin wannan aiki duk da gayyatar da gwamnatinsa ta yi masa.
“Na nemi Shell ya zo ya gudanar da shi kuma Shell ya ce ba za su yi ba. Na ce, ‘Don Allah ku zo ku yi adalci.’ Suka ce a’a. Na ce ‘lafiya, ku zo ku gudanar da shi, suka ce a’a,” inji Obasanjo.
Tsohon shugaban ya ci gaba da yin ƙarin haske kan tattaunawar da ya yi da shugaban kamfanin Shell, wanda ya kawo dalilai da dama na ƙin amincewa da kamfanin. Ya ce aikin Shell tun da farko shi ne samar da mai, ba tacewa ba, kuma matatun mai a Nijeriya sun yi kaɗan bisa ƙa’idojin duniya.
“Ya ce matatun man namu sun yi kaɗan sosai: Ganga 60,000, ganga 100,000, kuma ina tsammanin ganga 120,000. A wancan lokacin, matsakaita matatun mai yana zuwa ganga 250,000,” inji Obasanjo.
“Cin hanci da rashawa ya yi kaca-kaca a ayyukansu, wanda ya sa Shell ke shakkar shiga harkar.”
Bayan ƙin amincewa da Shell, Obasanjo ya koma ga hamshaƙin ɗan kasuwan Nijeriya kuma attajirin Afrika, Aliko ɗangote, wanda ya haɗa tawaga don ba da mafita. A cewar Obasanjo, Dangote ya biya kimanin Dala miliyan 750 don wani shiri na haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu (PPP) don gudanar da ayyukan matatun.
“Aliko ya samu wata tawaga kuma sun biya Dala miliyan 750, domin su shiga harkar PPP wajen tafiyar da matatun man. Magaji na ya mayar musu da kuɗaɗensu, na je wurinsa na yi masa bayanin abin da ya faru, amma ya ce kamfanin NNPC na son tafiyar da matatun, yana mai cewa za su iya sarrafa su,” inji Cif Obasanjo.
Duk da haka, Obasanjo ya bayyana ƙwarin gwiwa kan yadda ɗangote zai iya tafiyar da matatun mai na sa masu zaman kansu, inda ya bayyana cewa matatun mai da gwamnati ke gudanarwa sun gaza yin aiki yadda ya kamata.
“Ba da daɗewa ba aka gaya min cewa tun daga wancan lokacin an ɓarnata sama da dala biliyan biyu a matatun man, kuma har yanzu ba za su yi aiki ba,” inji Obasanjo.
“Idan kamfani kamar Shell ya gaya mani abin da suka gaya mini, zan yarda da su. Idan wani ya ce maka yanzu yana aiki, me ya sa suke tare da Aliko? Kuma Aliko zai yi nasa aikin matatar mai; ba wai kawai ya yi aiki ba, zai sa ya isar da shi.”
Ya ƙarƙare da karin maganar Yarbawa, inda ya kwatanta zarge-zargen da gwamnati ke yi game da matatun mai da alƙawurran yaudara.
