Daga SANI HAMAD GIWA a Abuja
A ranar Talatar da ta gabata ne Jamhuriyar Benin ta gayyaci jami’in diflomasiyyar Jamhuriyar Nijar bayan zargin da shugaban mulkin sojan Jamhuriyar Nijar, Birgediya Janar Abdourahamane Tchiani, ya yi na cewa, ƙasashe masu makwabta da Nijar suna goyon bayan ‘yan ta’adda a yammacin Afirka.
Benin dai na neman ƙarin haske daga jami’in diflomasiyyar ne bayan da Tchiani ya zargi ƙasar da zama magoya baya ga ‘yan ta’adda da kuma son tada zaune tsaye a Nijar.
Ministan harkokin wajen ƙasar Benin Olushegun Bakari ya aike da wasiƙar zanga-zangar a hukumance ga jami’in diflomasiyyar.
“Saboda zarge-zargen da ake yi wa ƙasarmu, an gayyaci jami’an tsaro na Nijar,” inji ma’aikatar harkokin wajen Benin a shafinta na ɗ.
Dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta yi tsami ne bayan juyin mulkin da sojoji suka yi da hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban Nijar Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.
Daga nan ne aka gwabza yaƙi a kan fitar da man da Nijar ke fitarwa ta gaɓar tekun Benin da kuma taƙaddamar buɗe kan iyakarsu, amma a cikin ‘yan watannin nan alamun sulhu ya ƙaru.
Ma’aikatar harkokin wajen Benin ta ce “Benin na ci gaba da jajircewa wajen tattaunawa da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.”
Kowanne daga cikin ƙasashen yammacin Afirka ya naɗa sabon jakada a ɗaya ɓangaren. An kuma saka Nijeriya a cikin ƙasashen da ke ƙoƙarin tada zaune tsaye a Nijar.
Tchiani, wanda ya yi wannan zargin a wata tattaunawa ranar kirsimati, ya bayyana cewa ana shirin kafa sansanin soji na Faransa a Nijeriya.
Nan take mai bai wa Nijeriya shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya yi watsi da hakan, inda ya bayyana cewa ƙasar ba za ta taɓa ba da damar samun sansanin soja na ƙasashen waje a ƙasarta ba.
A halin da ake ciki, gwamnatin tarayya ta ce a shirye take ta tattauna da Nijar.
A cikin wata sanarwa da ministan harkokin wajen ƙasar Yusuf Tuggar ya fitar, ya ce Nijeriya ta zaɓi tattaunawa ne a matsayin ginshiƙin samar da mafita mai ɗorewa kuma ba za ta ɗauki duk wani mataki da zai gurgunta ‘yancin kan Nijar, tsaro, da yankunanta, bisa ƙa’idojin ECOWAS.
Ministan ya jaddada aniyar Nijeriya na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yammacin Afirka, inda ya ce Nijeriya da Nijar a matsayin ƙasashe makwabta da kuma ‘yan uwan juna suna da alaƙa mai zurfi ta tarihi, al’adu da tattalin arziki.
