Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Ma’aikata da masu kamfanoni a rukunin ƙananan masana’antu na Dakata sun zargi kamfanin rarraba wuta na KEDCO da yunƙurin kassara musu sana’o’i i da suke ta ƙin ba su wuta da hakan ya jawo musu ɗimbin asara da kuma rasa aikin yi a tsakanin matasa.
Wannan ta sa ma’aikata a rukunin ƙananan masana’antun na Dakata suka gudanar da sallah da addu’o’i domin neman ɗaukin Ubangiji ya yi musu maganin duk wanda yake da hannu domin a kassara sana’ar ta su.
Taron addu’ar da aka gudanar a rukunin ƙananan masana’antu a safiyar Laraba ya samu halartar ɗimbin leburori da masu masana’antu da suka yi mutuƙar nuna ɓacin ransu na rashin basu wuta da kuma neman ɗauki daga duk masu ruwa da tsaki domin dafa musu wajen samun sauƙi wannan matsala.
Surajo Musa, ɗaya daga cikin shugabanni a ɗaya daga rukunin masana’ntun na Dakatar ya ce sun shiga wani yanayi mai wuya sakamakon rashin wuta da suke fama da shi a ƙananan masana’antun, sun doshi sama da kwanaki 90 ba cikakkiyar wuta da hakan ya jawo musu koma baya sosai sakamakon mutane da yawa anan suke samun na abinci ga yanayin matsanancin rayuwa da ake a ciki.
Ya ƙara da cewa mutane sakamakon rashin wutar da zasu yi aiki an shiga mummunan yanayi wasu ma sun zama kamar sun zautu wasu sun shiga wani yanayi har suna taɓa kayan wani, wanda baya maula ya shiga yi.
Ya nuni da cewa bayan an sami matsala ta wuta da ta shafi Arewa an dawo ana samar da wutar ta hanyar Jos take baiwa masana’antu, amma sai KEDCO suka ware wasu masana’antu suke basu suke ta hana ƙananan masana’antun Dakata sun nemi dalili da ake hana su wutar, sun ce wutar tana ɓata ne , amma da sukayi bincike da kansa Manajan Darakta na KEDCO ya tabbatar musu ba a ɓangaren su wutar take ɓata ba, sun gano inda take ɓata.
Ya ce amma duk da haka sai ya haɗa ya yi musu kuɗin goro baki ɗaya sun kuma turza a dawo musu da wutar ,amma yaƙi har sun nemi ɗaukin shugaban ma’aikatan Gwamnatin da Kwamishinan kasuwanci sun zauna dashi amma baya ba su wutar yanda yakamata sai ta awa biyu da ba za ta isa su yi aiki ba, sannan kuma su caje su a tsarin “Ban A” kuɗin mI yawa wannan kuma zalunci ne.
Surajo Musa yace yanzu har ta kai ga masu jari sun cinye ƙananan leburori babu aiki it kuma Gwamnati ta kau da kai daga gare su duk da taimakawa da suke na samar da ayyuka gà ɗinbin matasa an kyale su a halin da basu taɓa tsintar kai ba.
Shi ma Alhaji Murtala Isa Sadauki mai Kamfanin mai da roba a Dakata, ya ce leburorin sune suka shirya taro na addu’ar Alaunutu saboda suna ganin da su fito su yi zanga-zanga sai suka zaɓi su shirya addu’oi domin sun ga yanda masu masana’antu suke riƙe dasu da kima da daraja suka samar musu da aiki sun tabbatar ba su da laifi wajen rashin yin aiki.
Ya ce suna zargin mutum ɗaya ne a kamfanin KEDCO Abubakar Yusuf wanda shine manajan Daraktan yake neman saka dubban leburori cikin masifa. Suna zarginsa ne saboda sun za ci aiki yake da ya kamata su ba shi duk wani goyon baya a kungiyar su ta kananan masana’antu na Dakata sun gayyato shi su zauna dashi domin su fahimci juna amma yaƙi zuwa, suka nemi ya ba su dama su same shi bai yarda ba, har sai da suka sami shugaban KEDCO maji daɗin Gumel sannan ya bashi umurni ya zauna da su, a yayin zaman har sai da suka gayyato shugaban ma’aikata na Kano aka cimma matsaya, amma duk da haka manajan daraktan na KEDCO yaƙi yi musu abinda ya kamata yaƙi kunno wutar da zaman da suka yi yau kwanaki sama da 15 kenan duk maslaha da za a yi an yi.
Murtala Isa Sadauki da aka fi sani da Alaramma, ya ce abin lura KEDCO ba ita take da doka ba, doka tana nan a matsayinta na doka yakamata ya zama me bin ta ,idan yana zargin sun yi masa laifi ya kai su hukumar da Gwamnati ta tanada na kai ƙorƙfi, amma bai kai su ba, domin suma da suka zarge shi da wani laifi a baya can suka kai shi ta yi musu hukunci, wannan ya nuna suna zargin yana da wani ra’ayi na son zuciya na rusa tattalin arzikin Jihar Kano kenan.
