Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin iyali na jaridar Blueprint Manhaja. Muna godiya da bibiyar mu da ku ke yi.
A wannan makon za mu tattauna ne kan tasirin gara a aure, da kuma matsayin da take da shi ga al’ummar Ƙasar Hausa, da kuma bayanai kan matsayin gara a aure a mahanga ta magabata.
Idan muka yi maganar gara a nan muna magana ne kan kayan da ake kai wa gidan wanda aka aura bayan an kai amarya a matsayin tukuici ko nuna isa ko nuna ƙimar ɗiyar da danginta suka bada auren nata.
Ita garan takan zo ne daidai da al’adar masu yin ta, saidai mafi akasari kayan abinci ne da kuma na motsa baki kamar cincin, alkaki da sauransu. Kuma akan sanya kayan haɗa abincin, kamar su magi, dadawa, kuɓewa da makamantansu.
Idan mun ɗauke gara a mahanga ta ido, za mu iya cewa abu ne mai kyau duba da yadda garan kan taimakawa miji wurin ciyar da shi kafin ya farfaɗo daga ɗawainiyar biki da ya yi. Saidai za mu iya aibata gara idan muka buɗe ido sosai wurin ganin yadda iyayen yarinya ke matsanta kansu wurin ganin sun kai kayan na gani na faɗa, don gujewa reni.
Su kuwa a ɓangaren miji shirye suke su aibata garar da za a kawo masu matuƙar ba ta kai yadda suke tsammanin ta ba. Kuma ita kaɗai garar ta isa ta kawo gagarumin saɓani tsakanin dangin biyu.
Idan zan yi amfani da waɗannan hujjojin biyu, zan iya cewa gara wata babbar makami ce da sheɗan ke amfani da ita wurin yaƙar zaman lafiyar aure. Domin kuwa ta dalilinta kawai za a iya kafa ƙiyayyar da za ta iya kai har ga ‘ya’ya ta hanyar yawan yi wa uwarsu gorin rashin gara.
Abinda masu wannan ɗabi’ar ba su sani ba, ko suka manta, ba ta inda addini ya shar’anta wa mace bayar da wani abu na daga abinda za a ciyar da ita da shi, ko bayar da tukuicin aurenta da aka yi. Ciyar da mace haƙƙi ne na mijinta, ciyar da iyayenshi ko danginci bai taɓa zama kan matarshi koda kuwa na rana ɗaya ne.
Da wannan zan iya cewa duk da akwai alkhairi a yin gara zan iya cewa barin ta zai fi alkhairi fiye da yinta. Idan kuwa ta zama dole a yi, to a yi ta bisa ga iyawa. Su iyayen yarinya su yi don taimakawa surukinsu, don haka za su yi ne iya ƙarfinsu. Shi kuwa kada ya sa rai, idan sun bayar ya gode.
Amma idan nawa ra’ayin ne zan ce a bar shi gabaɗaya, duk abinda ku ke da niyyar kai wa a matsayin gara, ku haɗa shi ku yi wa ‘yarku jari, ta nan za ta iya taimakon mijinta da ɗan abinda take samu.
Ku kuwa dangin miji masu jiran akawo maku gara, har da sa ran mai yawa don ɗan uwanku ya yi bajinta a lefe, in tambaye ku, shin da ya kai lefe ba a kawo kayan ɗaki ba? Duk da cewa su ma taimako ne, domin haƙƙi ne da ya rataya kansa shi mijin kamar yadda tufatar da ita ma yake kansa.
Na san da yawa za su iya aibata rubutuna a ƙoƙarinsu na nuna muhimmancin gara da suka ce ta samo asali daga magabata, don haka za mu yi waiwaye kan hujja da inda masu yin al’adar gara suke fakewa a matsayin ta samu asali daga addini.
Shin gara na da matsuguni a cikin addini?
Za mu ci gaba a mako mai zuwa, da yardar mai dukka.
