Wasu malamai sun koka akan gwamnatin tarayya domin sanya hannu akan Yarjejeniyar nan mai cece kuce ta Samoa.
A cewar su, Yarjejeniyar tana ɗauke da wasu sharaɗai da suka ƙunshi cewa ƙasashe masu tasowa dole su yarda da yancin, yan luwadi, da yan maɗigo da yancin masu auren jinsi ɗaya.
Yarjejeniyar an samar da ita a tsibirin Samoa, nan aka sanya hannu a 15 ga watan Nuwamba 2023. Amma tun lokacin Yarjejeniyar ke samun suka daga addinai da dama wanda hakan ya saɓawa al’adunsu.
Bayanai akan Yarjejeniyar ya fito ne lokacin da ministan kasafin kuɗi da tattalin arziki Alhaji Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana irin cigaba da ake samu, a wata liyafa da kungiyar ƙasashen turai suka shirya a Abuja. Duk da dai yace,Najeriya ta sa hannu ne a sashin bashin dala biliyan 150.
Ƙasashe da dama a duniya sun ƙi yarda sun sanya hannu kan Yarjejeniyar a 2023 lokacin da aka yi ta. Ƙasashen sun haɗa da, Guinea, Trinidad and Tobago, Mauritania da wasu ƙasashen Afirka da dama.
Yanzu haka wannan lamari ya jawo cece kuce a shafukan sada zumunta na Najeriya inda yan Najeriya ke nuna Allah wadai da wannan cigaban.